A farkon makon nan ne Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sabbin ministocinsa guda 45 a fadarsa da ke Abuja tare da gargadin cewa ‘Yan Nijeriya na bin su bashin aiki tukuru cikin gaskiya da rikon amana a dukkan al’amuran da za su gudanar a ofisoshinsu.
Tinubu wanda ya taya wadanda aka nada ministoci murna, ya ce shi da kansa ya zabo su domin su taimaka masa tafiyar da harkokin gwamnatinsa, inda ya bukace su; su sanya ido sosai wajen sauke nauyin da aka dora musu.
A cewarsa, “Bisa yadda kundin tsarin mulki ya tanada, majalisar dattawan Nijeriya ta tantance tare da tabbatar da ministoci 4. Maza da matan da aka rantsar da su, na zabo su ne bisa irin rawar da suka taka da nasarorin da suka samu lokacin da suke rike da mukamai a gwamnati da bangarori masu zaman kansu.
“Kalubalen da muke fuskanta a halin yanzu na da matukar ban tsoro. Amma duk da haka, muna da damar aiwatar da gyare-gyaren da su inganta ayyukan gwamnati da bunkasa tattalin arzikin kasarmu da tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kuma wadata jama’armu.
“Wadannan su ne manufofin da ke tabbatar da jandarmu. Kuma wadannan su ne manufofin da suka zaburar da masu zabe har suka mince da mu.
“A matsayinku na ministocin tarayyar Nijeriya, ku ba ministocin wani yanki ba ne, ministocin Nijeriya ne gaki daya.
“Tun bayan rantsar da ni a ranar 29 ga watan Mayu, na dauki matakin fara aiwatar da ajandar da na yi yakin neman zabe. Bisa yadda na kaddamar da ministocin a yau, muna gab da kara habaka kokarinmu na gudanar da mulki mai inganci tare da bayyana kyakkyawan fata ga ‘yan Nijeriya. Komi zai tafi daidai ne bisa hadin kai, kuma na yi imani muna da shi a nan,” in ji Tinubu.
Sai dai kuma, tambayar da ‘Yan Nijeriya da dama suke yi ita ce, wace alkibla ce sabbin ministocin za su dosa? Ana iya yanke hukuncin bisa jawaban da suka gabatar a ranar farko da suka isa ma’aikatun da aka raba musu.
•Ministan Abuja, Wike Ya Lashi Takobin Ragargaza A Abuja
Sabon ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya lashi takobin ragargaza a Babban Birnin Tarayya Abuja yayin da ya gargadi masu karkatar da tsarin Abuja ta hanyar yin gine-gine ba bisa ka’ida ba.
Wike ya ce, “Idan san ka yi gini inda bai kamata, za mu ruguje shi. Ko kai minista ne ko jakada, idan ka san ka yi gini inda bai kamata ba, dole ne mu ruguje gidanka.
“Wadanda suka yi gine-gine kan magudanan ruwa ko wuraren ajiye motoci ko wuraren shakatawa dole ne mu ruguje su. Zan kwace filayen wadanda gwamnati ta bai wa domin bunkasa birnin tarayya, wanda tun ana sayarwa naira 200,000, yanzu ya kai biliyan biyu, amma ba a gina ba, to zan kwace irin wadannan filaye.
“Za mu karbe filayenmu tare da bai wa masu son bunkasa Abuja. Kuma dole ne ku sanya hannu kan cewa za ku gina a cikin karamin lokaci.”
•Zan Tabbatar Da Cewa Nijeriya Na Fitar Da Abinci Kasashen Waje – Ministan Noma
Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari ya ce zai tabbatar an samar da wadataccen abinci da zai ciyar da ‘yan Nijeriya da fitar da abinci zuwa sauran kasashen ketare.
Alhaji Kyari ya bayyana haka ne a wata gajeriyar liyafar da ma’aikatar ta shirya masa tare da karamin minista Aliyu Sabi Abdullahi a ranar Litinin.
Ya ce Nijeriya na fama da yunwa sakamakon ambaliyar ruwa da rashin tsaro suka haddasa, amma idan aka hada karfi da karfe za a shawo kan kalubalen.
“Mun san kalubalen da muke fuskanta a yanzu, yunwa na daya daga cikin manyan matsalolin da muke fama da su a kasar nan. Idan muka ce yunwa, muna nufin matsalolin da ke haddasa rashin samar da abinci kamar irin su rashin tsaro, ambaliya ruwa da sauransu.
“Ina ganin muna da babban kalubale, amma dai abin da ba za a iya magancewa ne. Burinmu ba wai don samar da tsaro da ciyar da kasa ba ne har ma da fitar da abinci zuwa kasashen waje wanda muke da wannan fata kuma za mu iya”.
•Harkokin Yawon Bude Ido Za Su Zama Hanyar Samun Kudaden Shiga – Ministar Bude Ido
Sabuwar ministar yawon bude ido, Misis Lola Ade-John, ta ce za ta yi aiki tare da ma’aikatun gwamnati, hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki don mayar da bangaren yawon bude ido ya zama babban hanyar samun kudaden shiga.
Ade-John ta bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da ta shiga a Abuja.
Ministar ta ce yawon bude ido ya shafi kasuwanci da hada kai da masu ruwa da tsaki, ta ce za ta hada kai da masu zuba jari da gwamnatoci da jama’ar gari domin inganta fannin.
“Akwai babban hanyar samun kudaden shiga a ma’aikatar yawon bude ido mutukar an inganta fannin.
“Idan na samu goyon bayan kowa da kowa, yawon bude ido zai zama hanyar farko da ake samun kudaden shiga a cikin gida da waje,” in ji ta.
•Za Mu Rika Fada Wa ‘Yan Nijeriya Gaskiya Game Da Ayyukan Gwamnati – Minastan Labarai, Malagi
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa zai gaya musu gaskiya game da manufofi da shirye-shiryen gwamnati a kowane lokaci.
Malagi ya bayyana haka ne a ranar Litinin a liyafar da aka shirya masa don karrama ministocin yada labarai da wayar da kan jama’a, ministan fasaha, al’adu da tattalin arziki da kuma ministan yawon bude ido a cibiyar yada labarai ta kasa a Abuja.
Ya ce ma’aikatar za ta bude hanyar hanyar gudanar da gaskiya da rikon amana a kan dukkan manufofi 0da shirye-shiryen gwamnati.
Ya ce: “Ina so in gaya muku duk cewa ni dan jarida ne mai bayar da rahoton. Shugaban kasa ya bukace ni da in zo in gaya muku cewa wannan sabuwar ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a ce.
“Yawancin shugabannin hukumomi a wannan ma’aikatar gaskiya abokaina ne domin na yi mu’amala da su na tsawon shekaru 20 zuwa 30 da suka wuce. Ina tabbatar muku cewa za mu sami sabuwar ma’aikatar yada labarai.
“Shugaban kasa ya aiko ni in zo in gaya muku gaskiyar lamari yadda abin yake. Taimakon kasa zai kasance jigon wannan ma’aikatar baya ga yada labaran da muka sani, ” in ji shi.
•Ya Kamata A Ware Kashi Daya Na Harajin Barasa Da Sigari Domin Kula Da Lafiyar Mata – Ministar Mata
Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta yi kira da a ware akalla kashi daya cikin dari na harajin barasa da sigari da sauran su domin kulawa da lafiyar mata, musamman a yankunan karkara domin rage yawan mace-mace a wurin haifuwa.
Ta bayyana hakan ne a lokacin da ta shiga ofis sa’ilin da take zantawa da manema labarai a Abuja.
Ta ce: “Muna bukatar wani abu a cikin harajin abubuwan da maza suka fi so, kamar barasa, sigari da sauransu, akalla kashi daya cikin dari domin kula da lafiyar mata, musamman a yankunan karkara wajen rage yawan mace-mace a lokacin haihuwa.”
Ta kuma bukaci sauran masu ruwa da tsaki da su tallafa wa gwamnati ta hanyar tsarin inshora da zai bai wa mata da kananan yara a yankunan karkara damar samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya.
Kennedy-Ohanenye ta ci gaba da ba da bayanin abubuwan da ma’aikatar za ta yi cikin kwanaki 100 don rage radadin da mata da kananan yara ke fuskanta, inda ta lissafo inganta harkokin kiwon lafiya da noma ga wadanda ke yankunan karkara da horar da mata a shiyyoyi shida na kasar nan domin samun sana’o’i daban-daban na inganta rayuwarsu da habaka kudaden shiga na kasa tare da dakile barace-barace a kan hanyoyi da rashin tsaro.
Zan Sake Farfado Da Fannin Ilimi – Minista Ilimi
Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya yi alkawarin sake farfado da fannin ilimi karkashin gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu ta hanyar kawo sauyi a fannin.
Mammna ya bayyana cewa, “Da yardar Allah, muna da niyyar yin aiki a lokacin wa’adin mulkinmu kuma ‘yan Nijeriya za su ga bambanci.
“Mun san yadda ma’aikatar ke da matukar muhimmanci. Ma’aikatar ce ke samar da lauyoyi da likitoci da injiniyoyi da sauran su. Idan har za mu iya daidaita al’amura, hakan zai kawo ci gabanmu,” in ji shi.
•Za Mu Tsamo ‘Yan Nijeriya Miliyan 133 Daga Kangin Talauci – Ministar Jin Kai
Sabuwar ministar harkokin jin kai, Misis Beta Edu ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin tsamo ‘yan Nijeriya miliyan 133 daga kanjin talauci.
Madam Edu ta bayar da wannan tabbacin ne a lokacin wata gajeriyar liyafar da ma’aikatar ta shirya bayan taron rantsar da ita da aka yi a fadar gwamnati da ke Abuja, wanda ya yi daidai da cika shekaru hudu da kafa ma’aikatar.
A cewarta, gwamnatin tarayya za ta iya cimma wannan burin ne kadai ta hanyar bayar da ayyukan jin kai da kuma shirye-shiryen rage radadin talauci.
“Babban abin da muka saka a gaba shi ne tsamo ‘yan Nijeriya miliyan 133 daga kangin talauci.
“Za mu iya yin haka ne a mataki-mataki, saboda lamarin yana da matukar karfi, babu abin da ba zai yiwu ba”, in ji ta.
“Haka zalika, muna da abokan hudarmu da za su taimaka wa mutane su ba da ayyukan jin kai a cikin kankanin lokaci.
“Mu ma, za mu samar da damar ga ‘yan Nijeriya, musamman ma matasa”.
Ministar wanda ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya kudurin da Shugaba Tinubu ya yi na sanya murmushi a fuskokin ‘yan Nijeriya.
•Tsaro Zai Inganta Nan Da Shekara Daya – Ministan Tsaro, Badaru
Ministan tsaro, Alhaji Mohammed Abubakar Badaru,ya bayyana cewa tsaro zai inganta nan da shekara daya.
Ya kuma hori hafsoshin tsaro da su gabatar da jadawali da abubuwan da suke bukata domin kawo karshen rashin tsaro a fadin kasar nan.
Badaru, wanda ya bayyana haka a hedkwatar ma’aikatar tsaro a lokacin da ya shiga ofis a matsayin ministan tsaro.
Ya ce aikinsa da na karamin ministansa da na hafsoshin tsaro na cikin hadari idan ba su kawo karshen rashin tsaro a shekara daya ba.
“Ba mu da wani dalili na gazawa, don haka ina so in gode wa duk wadanda ke nan tare da tabbatar musu da cewa za mu yi iya bakin kokarinmu wajen ganin mun kawar da kalubalen tsaro a kasar nan. Shugaban kasa da al’umma suna bin mu bashi. A matsayinmu na ‘yan siyasa, ba za mu dauki rashin nasara ba. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba, ba mu shirya amsar rashin nasara ba, kuma ba za mu gaza ba,” in ji shi.
Ya yi alkawarin ganawa da jami’an tsaro duk wata-wata domin inganta hadin kai wajen kawo karshen rashin tsaro.
•Zan Daga Martabar Nijeriya A Idon Duniya – Ministar Al’adu
Ministar al’adu da kirkiran tattalin arziki, Hannatu Musawa, ta ce ma’aikatar da ke karkashinta za ta sake daga martabar Nijeriya.
Ta ce, “Nijeriya ta kasance kasa mai girma.
“Lokacin da aka ce min an nada ni minista, babu wata ma’aikatar da nake son a tura ni kamar ma’aikatar al’adu da kirkiran tattalin arziki. A ko da yaushe ina sha’awar daukar wannan ma’aikatar zuwa matakin da ake bukata.
“Ni mawakiya ce kuma marubuciyar wake-wake. Don haka na fahimci tsarin kere-kere. Za mu sake daga martabar Nijeriya a duniya. Za mu mayar da Nijeriya kasa mafi girma a duniya.
” Mun fito ne daga kasar da ke da harsuna sama da 250, za mu yi amfani da shi wajen daga martabar Nijeriya ga duniya,” in ji Musawa.
•Duk Wata Hanya Da Za A Gina A Karkashina Za Ta Shekara 6 Ba Tare Da Gyara Ba – Umahi
Ministan ayyuka, Injiniya Dabid Nweze Umahi ya tabbatar wa masu amfani da hanyar cewa, a matsayinsa na ministan ayyuka zai tabbatar da ganin an gyara hanyoyin kasar nan domin amfanan daukacin ‘yan Nijeriya.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi na liyafar karrama shi da gwamnatin Jihar Ebonyi ta yi a Abuja.
Ministan ya yi alkawarin cewa ‘yan Nijeriya za su shaida kwazonsa, da jajircewa wajen bunkasa ababen more rayuwa a karkashin kulawarsa. Ya kara da cewa duk wata hanya da za a gina a karkashin jagorancinsa, za ta dauki fiye da shekaru shida ba tare da ta bukaci gyara ba.
•Ministan Harkokin Cikin Gida: Za Mu Sanya Na’urori Don Tsare Iyakokinmu
Ministan harkokin cikin gida, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na sanya na’urori don tabbatar da tsaron iyakokin Nijeriya yadda ya kamata.
Tunji-Ojo ya ce: “Muna bukatar tabbatar da tsaron iyakokinmu, kuma muna bukatar tabbatar da cewa an kare dukkan iyakokin kasa da ta sama da ta ruwa.
“Dole ne mu yi amfani da na’urori wajen habaka abubuwan da muka saba yi.
“Wannan wani abu ne da ya kamata mu yi. Shugaban ya umurci mu tabbatar da cewa mun kawo sauyi.”
Ya kuma yi alkawarin cewa za a duba batun biza da kuma fasfot domin tsaftace tsarin.
…Ministocin Tinubu 48 Za Su Lakume Naira Biliyan 8.6 Cikin Shekaru Hudu
Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta kashe naira biliyan 8.63 wajen biyan albashi da alawus-alawus na ministoci a cikin shekaru hudu masu zuwa, kamar yadda binciken jaridar Daily Trust ya nuna.
Alkaluman na iya karuwa yayin da Hukumar Kula da Harakokin Kudi ta Kasa (RMAFC) ta kammala nazari kan albashin ma’aikatan gwamnati.
Wannan dai shi ne karon farko da majalisar ministocin gwamnatin tarayya za ta kunshi ministoci 48 tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a kasar nan a shekarar 1999.
Wani binciken ya nuna cewa gwamnatin tarayya za ta kashe sama da naira biliyan 13 wajen biyan albashi da alawus-alawus na ministoci kadai.
Wannan adadin ya nuna cewa ainihin albashin minista shi ne naira 2,026,400 a duk shekara, kudin man fetur a shekara naira 1,519,800, kudin taimakansa naira 506,600, ma’aikatansa na gida naira 1,519,800, kudin shakatawa naira 911,880, kudin kayan aiki naira 607,920, kudin kula da kai naira 405,280 da kudin jaridu 303,960.
A bisa wannan bincike, kowanne daya daga cikin ministoci 48 zai samu albashin naira miliyan 31.2 na tsawon shekaru hudu. Wannan yana nuna cewa dukkansu za su karbi naira biliya 1.497 a matsayin albashi na wata-wata na shekaru hudu masu zuwa.
Ana kuma ba kowane minista karin alawus-alawus na shekara-shekara na naira miliyan 37.28, wanda ya kama zuwa naira biliyan 1.785 a duk shekara, sannan dukkansu kuma za a kashe musu naira biliyan 7.142 na tsawon shekaru hudu.