• English
  • Business News
Wednesday, July 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dabi’un Kankan Da Kai Na Manzon Allah S.A.W, Darasi Na Biyu

by Sulaiman and Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
2 years ago
in Dausayin Musulunci
0
Dabi’un Kankan Da Kai Na Manzon Allah S.A.W, Darasi Na Biyu
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Jama’a assalamu alaikum. Idan ba a manta ba, makonni uku da suka gabata mun kawo darasi na farko a kan dabi’un kankan da kai na Annabi (SAW), cikon ikon ba mu samu damar kawo kashi na biyu ba sai a wannan makon.

Kamar yadda muka yi bayani a darasi na farko, an karbo Hadisi daga Abi Umamata yana cewa, wata rana Annabi (SAW) ya fito zuwa gare mu yana dogara sanda, sai muka mike masa tsaye, sai ya ce mana (don kankan da kai), kar ku tashi kamar yadda wadanda ba Larabawa ba suke mike wa shugabanninsu, sashinsu yana girmama sashi, ni bawa ne, ina cin abinci kamar yadda bayi ke cin abinci, ina zama kamar yadda bawa yake zama.

  • Budi Da Cikar Ni’imar Allah Ga Annabi Muhammadu (SAW)

Malamai suka ce, Annabi (SAW) ya fadi wannan ne don kankan da kai ko kuma sabida ba al’adar larabawa ba ce. Malamai suka ce, kar ka mike wa wanda bai da wani alkhairi don girmamawa sai dai don tsoron sharrinsa, amma Sarki ko Shugaba ko Malami ko Mahaifi ko wani mai daraja, ka girmama shi da duk irin tsarin girmamawa na wannan al’ummar, sabida ranar yakin Khandaku da aka yaki Bani Kuraizah, wadanda suka ce sun yarda da hukuncin Sa’adu bin Mu’azu wanda shi kuma an harbe shi a kan babbar jijiya mai rike da rai, Annabi (SAW) ya sa aka dauko shi a kan Jaki sabida ba ya iya yin komai, da aka kawo shi sai Annabi (SAW) ya ce musu “Kumu ila sayyidikum, ku mike wa shugabanku”. Ta wannan hadisi aka samu hukuncin mike wa shugaba.

Akwai wakoki da dama da Hassanu ya yi wa Sahabbai kan mike wa Annabi (SAW).
“In mike wa Shugaba dole ne a wurina, in ki mike wa wannann shugaban, sam banga ya dace ba a wurina.”
‘yanzu mai hankali mai fahimta zai ga wannan kyawun ya ki mikewa?”
Annabi (SAW) ya kasance yana hawa Jaki, yana yin goyo ma a kan jakin, yana zuwa ya gaida Talakawa, yana zama da Talakawa, yana amsa kiran bawa, in bawa ya shirya wata Liyafa, Annabi (SAW) yana amsa gayyata, yana zama tsakanin Sahabbansa a duk inda zama ya tike masa.

A cikin Hadisin Sayyadina Umar, Annabi (SAW) yana cewa, kar ku yi min yabo na kai karshe wanda zai janyo ku wulakanta wani Annabi. Yabon Annabi (SAW) na Shari’a yana nan, shi bawan Allah ne, saninsa kuma na Ma’arifa yana nan (Rasulun minallahi…

Labarai Masu Nasaba

Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (2)

Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (3)

Manzo ne daga Allah), “Ni haske ne daga Allah, Mu’uminai kuma haske ne daga haskena” duk wannan yabon yana nan. Karshe dai, Shari’a wurinta daban, Ma’arifa wurinta daban. Amma babu wani Arifi da ya yarda ka fadi abin da ka sani na Ma’arifa a wurin ‘yan shari’a, sabida hadisin Annabi (SAW) ga sayyadina Umar “Umar ka san ko ni waye?”
“Kar ku ketare iyaka wajen girmama ni kamar yadda Nasara ta tsallake iyaka” su ma Nasara in maganar Ma’arifa suke yi, su tsaya can. Imam Garzali ya yi littafi mai girma kan wadannan maganganu da ya sa Nasara ta tsallake iyaka a cikin littafinsa mai suna ‘Sarihul Injili’.

Annabi (SAW) a cikin kankan da kai, ya ce wa Sahabbansa, in za ku yabe ni, ku ce min “Abdullahi – Bawan Allah”. Sufaye suna cewa, wannan kuma shi ne daidai a ma’arifa, don karshen Arifi abinda zai tarar shi ne ‘Abdu’ “Subhanallazi asra bi abdihi lailan…– tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiya da bawansa da daddare…”
An karbo daga Anas cewa, wata mace, Ummu Zafarin (kila mai yi wa Sayyada Khadijah kitso ce) tana da matsalar hankali kadan wani lokaci, ta zo ta ce wa Annabi SAW “ Ina da bukata a wurinka ya Muhammad” sai ya ce mata, “to zauna ya uwar wane (Annabi SAW ya yi mata alkunya, bai fada sunan danta ba ko kuma mai hadisin ya manta sunan dan da aka ambata), duk inda kike so in zauna in biya miki bukatunki a duk fadin garin Madina zan tsaya miki, ki zabi inda kike so mu zauna in ji bukatunki, ni kuma insha Allah zan yi miki duk bukatunki. Sannan ta zauna Annabi (SAW) shi ma ya zauna ta fada masa duk bukatunta. Manzon Allah (SAW) ya yi mata hakan ne a lokacin da Larabawa suke kin ‘ya’ya mata.

Anas dan Malik ya ce, Annabi (SAW) yana hawa Jaki, yana amsa kiran Bawa in ya gayyace shi, ranar yakin Bani Kuraizah, an ga Annabi (SAW) a kan jaki, an yi wa jakin linzami da ragama sannan jakin shimfida kawai aka yi masa.

Anas ya kara da cewa, ana gayyatar Annabi (SAW) zuwa walimar da za a ci gurasa da ake ci da kakiden da ya fara lalacewa sabida dadewa a ajiye. Malamai sabida wannan Hadisin suka yi fatawa, in mutane sun gayyace ka wurin taron al’adarsu suna da abinci mai wari, mara cutarwa kuma abincin mai girma ne a wurinsu, ba laifi kai ma ka hakura ka bi al’adar sabida girmama su.
Anas ya ce, Annabi (SAW) ya yi aikin Hajji a kan wani tsohon sirdin rakumi, an sa masa wata ‘yar katifa, da katifar da sirdin gaba daya ba su kai Dirhami hudu ba, amma kuma Annabi (SAW) sai aka ji yana addu’a yana cewa, Allah ka sanya wannan Hajjin karbabbiya wacce ba Riya a ciki. Sabida kankan da kai na Annabi (SAW), a kan tsohon sirdin rakumi ya yi aikin Hajji. Amma a wannan zamani ga mu nan, a jirage na alfarma, a dakunan Hotel masu sanyi da alfarma muke yi.

Wanann shi ne Annabinmu (SAW), wanda aka bude wa arzikin da ke kan kasa baki daya amma ya hau sirdin rakumi tsoho. Hadiyyar rakuma 100 ya bayar aka yanka a wannan Hajjin.

Yayin da aka bude masa Makkah, ya shiga Makkah da rundunar Musulmai, an ga ya sunkuyar da kansa kasa yana kan rakumi har sai da Gemunsa ya kusa taba sirdin rakumin da yake kai.

Yana daga cikin kankan da kai na Annabi SAW, fadinsa na cewa “La tufaddiluni ala Yunusa ibn Matta’a – kar ku fifita ni a kan Yunusa dan Matta’a”. Malamai suka ce, Annabi Yunusa (AS) sai da ya shiga duhun dare, cikin duhun Teku, cikin duhun Kifi sannan ya kai (Mushahada), shi kuma Annabi SAW an yi tafiyar dare da shi, aka je ‘dana fatadalla’ sannan ‘kaba kausaini au adna’ sannan ya yi Mushahada. Kila da Annabi (SAW) da Yunusa (AS) duk wuri daya suka je, shi ya sa ya ce kar ku fifita ni a kanshi. Amma in ba haka ba, Suratu Yakdin da ta kawo labarin Annabi Yunusa, Annabtarsa ma ba ta cika ba, yana da fushi “iz zahaba mugadiban fazanna allan nakdira alaihi, fa nada fizzulumat… – ka tina yayin da ya tafi cikin fushi ya yi zaton ba mu da iko a kansa, sai gashi yana kira a cikin duhu…”, don haka duk kissar Annabawa da Suratu Yakdin ta kawo, in an zo karshe sai ta ce aminci ya tabbata ga ‘yan gidan Annabin amma da ta zo kan Annabi Yunusa sai ta tsallake ayar aminci ga ‘yan gidansa sabida aikensa bai cika ba. Amma Shehu Ibrahim Inyass (RA) ya ce, ayar aminci ta karshen Surar ta riske shi “Wa salamun alal mursalin, wal hamdulillahi rabbil alamin”

Don haka, ba za a hada aiken Annabi (SAW) da na Annabi Yunusa ba, malamai suka ce, Mushahada ta Ma’arifa ake nufi a fadinsa na cewa “La tufaddiluni ala Yunusa ibn Matta’a – kar ku Fifita ni a kan Yunusa dan Matta’a”. Wanann Hadisin kuma, wa’azi ne ga Malamai a wurin taron Mauludi, Annabi (SAW) ya hana wulakantawa ko rashin ganin girman Annabawa wurin kwatanta su da shi (SAW), ba sai an wulakanta wani Annabi ba za a san girman Annabi (SAW), hasali ma, Kafirci ne wulakanta wani daga cikin Annabawa.
Allah tabaraka wata’ala cewa ya yi “Tilkar rusulu faddalna ba’adahum ala ba’adi… – wa ‘yancan Manzonnin, mun Fifita wasu a kan wasu.”

Akwai hadisai da Annabi (SAW) ya fada don kar a wulakanta sauran Annabawa da ake ganin kafarsu ta zame. Daga ciki akwai Hadisin Annabi Ibrahim (AS) da ya ce wa Ubangiji “nuna min yadda kake raya matattu don zuciyata ta nutsu” sai Annabi (SAW) ya ce “Mu muka fi cancanta da kokonto kan Ibrahim” kar a ce Annabi Ibrahim (AS) ya yi shakka kan lamarin Ubangijinshi sai (SAW) ya ce mu muka fi cancanta da mu ce zuciyarmu ta nutsu fiye da shi. Bambancin Annabi Ibrahim da Uzairu a kan irin wannan maganar shi ne, Annabi Ibrahim ya yi Imani sai dai yana son zuciyarsa ta nutsu, Uzairu kuma kokonto ya yi da cewa “ta kaka Allah zai raya matattu” sai Ubangiji ya buga misali a kanshi.

Manzon Allah (SAW) ya kara cewa, “Da na zauna a kurku kamar yadda Yusufu ya zauna, da sarki ya aiko yana kira na, da a guje zan tashi na amsa”. Wata rana Annabi (SAW) ya fada wa wanda ya kira shi da “Khairul bariyyati – fiyayyen halitta” sai ya ce “Annabi Ibrahim ne fiyayyen halitta” amma a hadisi ingatacce, Annabi (SAW) ya ce “Ana sayyidil Awwalina wal akhirina – ni ne shugaban na farko da na karshe”. Don haka, kowacce magana da mahallinta. Wata rana ana Fadar Jamala, wata rana ana Fadar Jalala, in ba ka da ilimin wannan ba dole sai ka yi magana a kan abin da ba ka sani ba.

An karbo Hadisi daga Sayyada A’isha da wasun sahabbai cikin siffanta Annabi (SAW), sun ce Annabi (SAW) a cikin gidansa yana cikin Hidimar iyalansa, yana gyara tufafinsa, yana tatsar akuyarsa, yana yi wa tufafinsa faci, yana dinke takalminsa, yana yi wa kansa hidima, yakan share dakinsa da kansa duk da yana da hadimai kuma suna yi masa hidima, yakan yi wa rakuminsa dabaibayi da kansa, yakan bai wa dabbobinsa abinci, yana cin abinci tare da hadimansa, in ya siyo abu a kasuwa yakan dauko kayansa da kansa.
An karbo daga Anas yana cewa, da yawa daga cikin kuyangun Madina za ka ga sun rike hannun Manzon Allah (SAW) suna tafiya tare da shi har zuwa inda suke nufi don biya musu bukatunsu.

Wani mutum ya taba shigowa wurin Annabi (SAW), sabida kwarjini sai makerketa ta kama Mutumin, sai Annabi (SAW) ya ce masa “sauwaka wa kanka, ni ba sarki ba ne, ni dan wata mace ne daga dangin Kuraishawa wacce take cin Kilishi.”


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Alkiblar Da Sabbin Ministoci Suka Dosa 

Next Post

Rusa Majalisar Zartarwa: Shugabannin NNPP Sun Yi Wa Kwankwaso Tutsu

Related

Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (2)
Dausayin Musulunci

Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (2)

4 days ago
Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (3)
Dausayin Musulunci

Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (3)

3 weeks ago
Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)
Dausayin Musulunci

Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)

4 weeks ago
Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (3)
Dausayin Musulunci

Darussan Hadisin Aikin Hajjin Manzon Allah S.A.W (2)

1 month ago
Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (3)
Dausayin Musulunci

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (3)

1 month ago
Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (1)
Dausayin Musulunci

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (1)

2 months ago
Next Post
Rusa Majalisar Zartarwa: Shugabannin NNPP Sun Yi Wa Kwankwaso Tutsu

Rusa Majalisar Zartarwa: Shugabannin NNPP Sun Yi Wa Kwankwaso Tutsu

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Dakon Kaya Na Tianzhou-9

Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Dakon Kaya Na Tianzhou-9

July 15, 2025
Ƙungiyar Buzaye Ta Yi Wa Nijeriya Ta’aziyyar Rasuwar Muhammadu Buhari

Ƙungiyar Buzaye Ta Yi Wa Nijeriya Ta’aziyyar Rasuwar Muhammadu Buhari

July 15, 2025
VFS Ta Ƙaddamar Da Cibiyar Yin Biza Zuwa Birtaniya A Kano

VFS Ta Ƙaddamar Da Cibiyar Yin Biza Zuwa Birtaniya A Kano

July 15, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabannin Tawagogin Kasa Da Kasa Masu Halartar Taron SCO

Xi Ya Gana Da Shugabannin Tawagogin Kasa Da Kasa Masu Halartar Taron SCO

July 15, 2025
An Gudanar Da Taro Game Da Sana’ar Sarrafa Sinadarai Na Kasa Da Kasa Karo Na 12 A Beijing

An Gudanar Da Taro Game Da Sana’ar Sarrafa Sinadarai Na Kasa Da Kasa Karo Na 12 A Beijing

July 15, 2025
Yawan Karuwar GDPn Sin A Rabin Farkon Bana Ya Kai 5.3%

Yawan Karuwar GDPn Sin A Rabin Farkon Bana Ya Kai 5.3%

July 15, 2025
Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 20, Sun Ƙona Gidaje A Ƙauyukan Filato

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 20, Sun Ƙona Gidaje A Ƙauyukan Filato

July 15, 2025
Shugaba Xi Ya Gabatar Da Jawabi Ga Taron Koli Game Da Aikin Raya Birane 

Shugaba Xi Ya Gabatar Da Jawabi Ga Taron Koli Game Da Aikin Raya Birane 

July 15, 2025
Ƴansanda Sun Cafke Mutane Biyu Bisa Zargin Kashe Ɗan Ƙasar China

Ƴansanda Sun Cafke Mutane Biyu Bisa Zargin Kashe Ɗan Ƙasar China

July 15, 2025
Taron Matasan Sin Da Afrika Kan Tsaro Zai Kirkiro Wata Sabuwar Mahanga Ta Magance Matsalolin Tsaro

Taron Matasan Sin Da Afrika Kan Tsaro Zai Kirkiro Wata Sabuwar Mahanga Ta Magance Matsalolin Tsaro

July 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.