Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana jin dadinta da ci gaba da aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Zariya, inda ta yi kira ga ma’aikatar ayyuka ta tarayya da ta gaggauta kammala aikin domin inganta harkar tsaro da ababen hawa da ke zirga-zirga akan hanyar.
Mataimakiyar gwamnan jihar, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe ce ta yi wannan kira a ranar Alhamis, 24 ga watan Agusta, 2023, yayin wata ziyarar ban girma da ministan ayyuka, Mista Nweze David Umahi, ya kai zuwa gidan gwamnatin jihar (Sir Kashim Ibrahim House).
Mataimakiyar gwamnan, ta roki ministan da cewa, gwamnati da al’ummar jihar Kaduna suna fata a ziyarar da zai sake kawo wa jihar don duba ayyukan karo na biyu, za a tabbatar an kammala aikin babban titin gabashin birnin jihar (Easten Bypass) – wanda aka fara aikin tun a shekarar 2002, aka sake sabunta kwantiragin aikin a shekarar 2017 wanda ake sa ran kammala aikin a 2021.
Tun da farko, Ministan ya bayyana cewa sun zo Kaduna ne akan umarnin da shugaban kasa ya ba su na rangadi a dukkan shiyyoyin jihar na majalisar dattawa don duba halin da ayyukan hanyoyin jihar ke ciki.
Umahi, ya kuma jaddada cewa, zuwan su Kaduna shaida ce da ke nuna irin muhimmancin da shugaba Tinubu ya baiwa jihar Kaduna.
A karshe, Ministan ya yabawa gwamnatin jihar Kaduna kan manufofinta na inganta jin dadin jama’arta Inda ya kara da cewa, duk da cewa gwamnatin sabuwa ce amma ta samu nasarori a bangarori da dama.