Ma’aikatar sufuri ta kasar Sin, ta bayyana yau Jumma’a cewa, a cikin watan Yuli, layin dogo na kasar Sin ya yi jigilar fasinjoji miliyan 409.19, wanda ya karu da kashi 80.9 cikin 100 kan na makamancin lokaci na shekarar bara.
A cewar ma’aikatar, a cikin watanni bakwai na farkon bana, tafiye-tafiyen fasinja ta layin dogo na kasar, ya karu da kashi 115.1 bisa 100, kan na bara, zuwa kusan biliyan 2.18. (Ibrahim)