Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) tare da hadin gwiwar gwamnatin Jihar Kebbi ta hanyar Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) sun ba da tallafin kayan agaji ga magidanta 22,202 da aka tabbatar a shekarar 2022 wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a fadin kananan hukumomi 21 na jihar.
An gudanar da bikin raba kayan tallafin a Bulasa a yau Juma’a a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.
- ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Tsohowar Shugaban Kotun Gargajiya A Benue
- Firimiyar Bana:Wasanni Uku Da Za Su Fi Daukar Hankalin Masu Kallo
Amma za a gudanar da raba kayan kan fuska biyu kuma za a fara kashi na farko a yau ga mutane 9,101 da abin ya shafa.
A nasa jawabin, Darakta Janar na NEMA Mustapha Habib, ya ce a shekarar 2022 an samu yawaitar ambaliyar ruwa a jahohin tarayya da dama kuma jihar Kebbi na daya daga ciki, bisa ga hakan ne aka hada da ma’aikatan NEMA tare da hadin gwiwar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kebbi SEMA aka tantance dukkanin iyalan da abin ya shafa a fadin kananan hukumomi 21 na jihar tare da tantance irin abin da suka rasa.
“Mun samu damar tantancewa tare da tantance iyalai 22,202 da abin ya shafa a ambaliyar ruwan shekarar 2022 a jihar Kebbi da gwamnatin tarayya sun amince da bayar da gudunmawar tallafin kayan agaji ga duk wadanda abin ya shafa a fadin kasar,” in ji shi.
Darakta Janar na NEMA, wanda ya samu wakilcin Alhaji Ismail Yusuf ya ci gaba da cewa, a wannan shekarar an tantance mutane 864,854 a fadin kasar amma kuma jihar Kebbi tana da mutane 22,202 da abin ya shafa.
Don haka a yau mun zo ne domin kaddamar da bikin raba kayan agajin da aka baiwa jihar Kebbi.
“Mun bayar da gudummawar kayayyakin agaji ga jihar Kebbi kamar haka: injin mika, keken dinki, katifa, mayafi, gidan sauro, bokiti, kayan girki, shinkafa da man Gyada. Sannan kayan aikin gona su sun hada da: irin shinkafa (Paddy Rice Seeds), maganin kwari, injinan ban ruwan shukka, zuwa ga dukkan iyalan da abin ya shafa da aka tabbatar da su” in ji shi”.
Ya kuma yi kira ga wadanda suka ci gajiyar tallafin a jihar da kada su sayar da ko daya daga cikin kayayyakin da aka ba su, wani abin jin dadi ne da gwamnatin tarayya ta ce ta yi domin ta tausaya muku tare da nuna damuwa kan abin da ya same ku.
A kan wannan bayanin, na yi kira ga dukanku da ku yi amfani da wadannan abubuwan ta hanyar da ya dace.
“Muna yi muku fatan alheri kuma za mu ci gaba da ba ku tallafi don samun damar ci gaba da gudanar da harkokin ku na yau da kullum, mun gode muku baki daya, muna kuma mika godiyarmu ga gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris da SEMA kan yadda suke ci gaba da gudanar da harkokin ku na yau da kullum. Haka Kuma ya yaba ga irin kyakkyawar alakar aiki da fahimtar juna a fannin gudanar da ayyukanmu na doka a duk lokacin da abin ya taso. Ya yaba.”
Da yake jawabi a wajen taron kaddamar da rabon kayan, Gwamna Nasir Idris wanda mataimakinsa Sanata Abubakar Umar Tafida ya wakilta, ya bada tabbacin ga gwamnatin tarayya da kuma shugaban hukumar NEMA wajen raba dukkan kayayyakin da aka bayar ga wadanda abin ya shafa a jihar Kebbi da yardar Allah ba tare da wata matsala ba, inji shi”.
Gwamnan ya ce “Tuni gwamnatin jihar ta kafa kwamitin da zai kula da rabon kayayyakin tare da tabbatar da an kai ga dukkan gidajen da aka tantance da ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar 2022 a jihar,” in ji shi.
Ya yi wa shugaban hukumar NEMA alkawarin cewa babu wani daga cikin wadanda abin ya shafa a jihar da zai sayar da duk wani kayan da aka bayar, domin wani bangare na aikin kwamitin shi ne tabbatar da cewa babu wanda ya sayar da kayansa da kuma lura da yadda ake amfani da shi.
Ya kuma bayyana cewa, dukkan kwamishinoni a kananan hukumomin da abin ya shafa,Mai su bada shawara ga gwamna , shugabannin kananan Hukumomi da kansiloli da sauran su za su kasance shugabannin kwamitoci da mambobin da aka dora musu alhakin tabbatar da duk kayayyakin da aka bayar ga wadanda abin ya shafa za su samu kayan su ba tare da karkatar da su ba, da kuma tabbatar da cewa sun yi amfani da su ta hanyar da ya dace, bisa ga hakan ya yi gargadin cewa kayayyakin su kai ga wadanda abin ya shafa”.
Haka zalika, ya yi kira ga wadanda suka ci gajiyar tallafin da su tabbatar da yin amfani da duk kayayyakin da aka ba su ta hanyar da ya dace tare da ci gaba da marawa gwamnatin tarayya da jihar k6ebbi baya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tunibu da Dakta Nasir Idris goyon bayan.
Bugu da kari ya ce karin tallafi da abubuwan jin dadi za su same ku nan ba da jimawa ba, don haka ku ci gaba da amince da gwamnatin domin tana da tsare-tsare masu yawa zuwa gare ku.
Daga karshe ya bayyana jin dadinsa bisa tallafin kayan agaji ga jiharsa da kuma ‘yan uwa da abin ya shafa, mun godewa gwamnatin tarayya da kuma Darakta Janar na NEMA bisa tallafin da suke bai wa jihar Kebbi.