Kotun sauraren shari’ar zaben Gwamnan Jihar Sakkwato za ta yanke hukuncin shari’ar zaben a watan Satumba a shari’ar da Sa’idu Umar da Jam’iyyar PDP suka shigar na kalubalantar zaben Gwamna Ahmed Aliyu Sokoto na jam’iyyar APC.
Bayan saurare tare da karbar rubutattun hujjojin karshe daga dukkanin bangarori a ranar Asabar, tawagar alkalai uku a karkashin jagorancin Haruna Mshelia sun adana ranar yanke hukuncin wanda suka ce za a bayyana ranar a cikin watan Satumba.
- Shugaban Burundi: Sin Tana Son Hada Kai Da Kasar Burundi
- APC A Jihar Kano Za Ta Yi Taron Addu’a Don Neman Nasara A Kotu
Mai kara, Sa’idu Umar da jam’iyyar PDP suna kalubalantar zaben Gwamna Ahmed Aliyu da Mataimakinsa, Idris Muhammad Gobir na jam’iyyar APC a bisa ga rashin takardu da sabawa dokokin zabe a zaben Gwamna na 18 ga watan Maris.
A zaman kotun, jagoran lauyoyin masu kara, Aare Olumuyiwa Akinboro SAN ya bukaci kotun da ta yi la’akari da hujjoji da shaidun da suka gabatar daga wakilan jam’iyya wadanda suka tabbatar da sabawa dokokin a zaben wanda aka gudanar cike da tashin hankali.
Akinboro ya ce musamman hujjojin da suka gabatar wadanda suka nuna bambace- bambance a tsakanin satifiket din makarantar sakandire ta Gwamna Aliyu da na jami’a wadanda sun bambanta da wadanda ya gabatar a Hukumar Zabe.
Lauyan ya kuma bukaci kotun da ta yi la’akari da kundin rajistar makarantar Town Primary School, Sabon- Birni daga 1986 -1987 da kuma takarda daga makarantar.
Ya yi bayanin dukkanin makarantun da ke da rajsita a Karamar Hukumar Sabon-Birni daga Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da Hukumar Ilimi da sauran hujjojin da ya bukaci kotun ta yi nazari.
Ya ce babu wani bayanan Gwamnati da ya nuna akwai wata makaranta mai suna Town Primary School kamar yadda Gobir ya ce ita ce makarantar da ya kammala kuma ta bashi satifiket.
Haka ma Akinboro ya bayyana cewar masu kara sun yi kokarin gamsar da kotu da hujjoji ta yadda shaidu 32 da suka kunshi jami’an Hukumar Zabe, Shugaban jam’iyyar PDP, shugaban makamai na Town Primary School Sabon-Birni da sauransu sun bayyana a gaban kotun sun kuma gabatar da takardu.
Ya ce a bisa ga hujjojin da suka gabatar, masu kariyar ba su cancanta da shiga zaben ba a bisa ga rashin takardu, don haka an yi kuskuren ba su kuri’u. A kan wannan ya bukaci kotun da ta yi watsi da kuri’un Ahmed Aliyu ta kuma tabbatar da Sa’idu Umar a matsayin wanda ya samu nasara a zaben Gwamna na 18 ga Maris 2023.
Shi kuwa lauyan APC, Hassan Liman SAN ya kalubalanci batun bambancin suna wanda ya ce ba ya hana dan takara shiga zabe don haka a cewarsa tsara sunan Gwamna Aliyu ba illa ba ce a takardunsa.
Lauyan ya bukaci kotun da ta yi watsi da karar tare da tabbatar da zaben Gwamna Ahmed Aliyu da Mataimakinsa Idris Gobir.