Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da wani muhimmin jawabi a kwanan baya, yayin taron tattaunawa tsakanin shugabannin kasar Sin da na kasashen Afirka, wanda ya yi matukar jawo hankalin bangarori daban daban na nahiyar Afirka, inda suka jinjinawa dabarun da shugaba Xi ya gabatar, na taimakawa dunkulewar kasashen Afirka, da tabbatar da babban aikin zamanantar da nahiyar, kuma suna cike imanin cewa, za a ciyar da huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka gaba zuwa wani sabon mataki.
Game da hakan, shugaban jam’iyyar gurguzu ta kasar Zambiya Fred M’membe, ya bayyana cewa, ya amince da ra’ayin Xi, game da ingiza ci gaban tsarin kasa da kasa bisa adalci, saboda hakan zai tabbatar da ci gaban tattalin arziki, da muhallin zaman lafiya a fadin duniya.
A nasa bangare kuwa, jakadan kasar Afirka ta Kudu dake kasar Sin Siyabonga C. Cwele, cewa ya yi shugabannin kasar Sin, da na kasashen Afirka suna mutumta junansu, don haka suna iya tsai da kuduri tare, domin sa kaimi ga ci gaban kasar Sin da Afirka, gami da dukkan kasashe masu tasowa baki daya. Ya ce yanzu karin kasashe masu tasowa za su shiga kungiyar BRICS, lamarin da zai taka rawar gani ga ci gaba, da wadatar kasashe masu tasowa, da ma daukacin kasashen duniya.
Shi kuwa shugaban kasar Senegal Macky Sall, cewa ya yi shugaba Xi Jinping, aboki ne ga al’ummomin kasashen Afirka, kuma yana farin cikin ganin kasashe da dama, na nuna fatansu na shiga tsarin BRICS, kuma ko shakka babu, tsarin hadin gwiwar BRICS din zai bunkasa bisa shigar sabbin mambobi. (Mai fassara: Jamila)