ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, September 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hadin Gwiwar Kasashen Afirka Da Kasar Sin Abin Koyi Ne

by CMG Hausa
3 years ago
Afirka

Wani babban burin da kasashe masu tasowa suka sanya a gaba shi ne ci gaban tattalin arziki, da zamanantar da kasa. Sai dai a karkashin tsarin kasa da kasa da kasashen yamma suka kafa, abu ne mai wuya a cimma wannan buri. Abun da ya faru a janhuriyar Nijar, wani misali ne a wannan fanni. Inda ko da yake akwai cece kuce game da tasirin juyin mulkin da aka yi, al’ummar kasar sun bayyana ra’ayinsu sarai yayin da suke zanga-zanga. Sun ce: “A kasarmu akwai ma’adinai iri-iri. Ga zinariya, da Uranium. Amma me ya sa muke ci gaba da fama da talauci? ” A ganinsu wasu manyan kasashe dake yammacin duniya ne suke da alhakin hakan, saboda babban batun da ya hana Nijar samun ci gaba shi ne tsarin kasa da kasa da su kasashen yamma suka tanada.

Sai dai ta yaya za a iya daidaita wancan tsohon tsarin? To, don cimma wannan buri, dole ne a dogara kan hadin gwiwar kasashe masu tasowa.

  • Sin Ta Bunkasa Fasahar Sarrafa Dumin Makamashin Nukiliya Domin Samar Da Haske Makamancin Na Rana

A wajen taron kolin tsarin BRICS da ya gudana a kwanan baya a kasar Afirka ta Kudu, dumbin kasashe masu tasowa sun nuna karfinsu sosai, inda suka cimma matsaya daya kan wasu manyan batutuwa da yawa, tare da nuna cewa, ta hanyar hadin gwiwa, kasashe masu tasowa za su iya biyan bukatun juna, da daidaita tsare-tsaren kasa da kasa, da neman samun karin ikon fada a ji a duniya, gami da tabbatar da moriyarsu ta bai daya. Kana taron tattaunawar shugabannin kasashen Afirka da kasar Sin, da shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa suka jagoranta, wanda ya gudana a gefen taron kolin BRICS, ya nuna wani hali mai inganci na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, inda ake girmama juna, da rufa wa junansu baya, da nuna sahihanci, gami da neman samun hakikanin sakamako.

ADVERTISEMENT

A wajen taron BRICS na wannan karo, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sha aiki sosai. Inda a cikin wa’adin taron na kwanaki 3, ya gana da shugabannin kasashen Afirka ta Kudu, da Senegal, da Habasha, da na sauran kasashe 4 dake nahiyar Afirka. Daga bisani a wajen taron shugabannin Afirka da na kasar Sin, shugaban ya tattauna tare da manyan shugabanni 12, da suke wakiltar kasashe, da kungiyoyin shiyyoyi, duk a nahiyar Afirka. Ta Haka, za a iya ganin yadda shugaban ke kallon kasashen Afirka da muhimmanci matuka.

Sa’an nan, idan mun yi tsokaci kan jawabin da shugaba Xi ya yi a wajen taron tattaunawar, gami da wata hadaddiyar sanarwar da mahalarta taron suka gabatar a hadin gwiwarsu, za mu san da cewa, kasashen Afirka da kasar Sin suna da bukatun iri daya, wato dukkansu na neman zamanintar da kasashensu, da wani tsarin kasa da kasa mai adalci, da zaman lafiya da kwanciyar hankali, gami da wani muhallin tattalin arziki na bude kofa, inda ake lura da moriyar kasashe daban daban. Hakan ya nuna tushe mai karfi na yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da kasar ta Sin.

LABARAI MASU NASABA

Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin

Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”

Ban da haka, za mu iya ganin yadda kasashen Afirka da kasar Sin suke girmama juna, da kokarin rufawa junansu baya. A wajen taron tattaunawa na shugabannin kasashen Afirka da kasar ta Sin, bangaren kasar Sin ya ce yana goyon bayan yunkurin kasashen Afirka na dunkule kansu waje guda, da mai da kungiyar AU daya daga cikin mambobin kungiyar G20. Kana kasar Sin ta yi alkawarin hada tsarinta na raya kasa, tare da na kasashen Afirka. Yayin da a nasu bangare, dimbin shugabannin kasashen Afirka da suka halarci taron sun jinjinawa kasar Sin, kan yadda ta gabatar da shawarwari na tabbatar da ci gaban tattalin arziki, da tsaro, da ci gaban al’adu a duniya, da zummar yada manufar kasancewar mabambantan bangarori masu fada a ji a duniya. Ta la’akari da yadda aka dade ana zama a karkarshin wani tsarin kasa da kasa da kasashen yamma suka kafa, za a bukaci jan hali da basira, don nacewa kan bin wata turbar da aka zaba da kai, da kokarin neman samun nasarori, gami da samun goyon baya daga abokan hulda.

Kana wasu shirye-shirye da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar a wajen taron, wadanda suka shafi yadda kasar Sin za ta taimaki kasashen Afirka raya bangarorin masana’antu, da aikin gona, da horar da ma’aikata, sun nuna takamaiman matakan da kasar Sin za ta dauka, don biyan bukatun kasashen Afirka a kokarinsu na zamanintar da kasa. Hakan ya nuna gaskiyar huldar hadin kai da ake samu tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin, inda ake lura da bukatun da ake da su, da kokarin cika alkawari, maimakon tsayawa kan kalmomin baka.

A ganin duk wata kasar dake kan hanyar tasowa, ba wani abun da ya fi damun ta, sama da yadda za a hana ta samun ci gaban tattalin arziki. Sai dai wani albishir da muka samu shi ne, kasashe masu tasowa sun riga sun fara samun cikakken karfi, inda za su iya samar da gyare-gyare kan tsare-tsaren kasa da kasa, ta hanyar yin hadin kai a tsakaninsu. Kana hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Afirka da kasar ta Sin abin koyi ne a wannan fanni, ga sauran kasashe masu tasowa. (Bello Wang)

Afirka
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin
Daga Birnin Sin

Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin

September 13, 2026
Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”
Daga Birnin Sin

Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”

September 13, 2026
Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi
Daga Birnin Sin

Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi

September 12, 2026
Next Post
Rasha Ta Kakkabo Jirage Marasa Matuka Na Ukraine

Rasha Ta Kakkabo Jirage Marasa Matuka Na Ukraine

LABARAI MASU NASABA

An Samu Babban Sakamako Kan Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Na Duniya

An Samu Babban Sakamako Kan Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Na Duniya

September 13, 2026
Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin

Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin

September 13, 2026
Afirka

An Gudanar Da Sallar Zana’idar Tsohon Gwamnan Gongola

September 13, 2026
Yajin Aikin ASUU: Malaman Jami’ar Jihar Kaduna Sun Bijirewa El-rufa’i

Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Ƙarin Albashi Ga Ma’aikatan KASU

September 13, 2026
Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

September 13, 2026
Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”

Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”

September 13, 2026
Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

September 13, 2026
Doma United Na Cigaba Da Jan Zarenta A Firimiyar Nijeriya Bayan Doke Enyimba

Doma United Na Cigaba Da Jan Zarenta A Firimiyar Nijeriya Bayan Doke Enyimba

September 13, 2026
Hafsat Bakari Ta Sake Dawo Da Sarƙaƙƙen Al’amari

Hafsat Bakari Ta Sake Dawo Da Sarƙaƙƙen Al’amari

September 13, 2026
Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa

Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa

September 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.