Majalisar amintattu (BoT) ta jam’iyyar NNPP ta dakatar da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na tsawon watanni shida daga shiga harkokin jam’iyyar bisa zarginsa da kasance cikin masu yi wa Jam’iyyar zagon kasa (anti-party).Â
BoT ta zargi Kwankwaso da rabar shugaban kasa Bola Tinubu, PDP da dan takararta, Atiku Abubakar, da dan takarar shugaban kasa na LP Peter Obi, ba tare da amincewar majalisar ba.
Kazalika, majalisar ta kuma warware wa Kwankwaso kambun kasancewa jigon jam’iyyar na kasa da na jiha.
Kazalika, ta rushe dukkanin mambobin ayyuka (NWC) na jam’iyyar tare da nada sabbi a matsayin na riko karkashin jagorancin Dr. Agbo Major, da Kwamared Ogini Olaposi a matsayin sakataren riko tare da wasu jagorori 18 na jam’iyyar a matakin kasa.
Majalisar ta ce ta rushe tsohowar NWC dinta ne saboda rashin iyawa da gazawa da aka samu daga mambobin kwamitin ayyukan.
A jawabin bayan taron da suka gudanar a ranar Talata a Apapa, Legas da shugaban BoT na jam’iyyar, Temitope Aluko, ya fitar ya ce, “An yi ta kwaskwarima wa kundun tsarin mulkin NNPP ba tare da bin matakan da suka dace ba, kawai wasu daidaiku ne ke dagula lamura.”
Kazalika, majalisar ta gargadi Alhaji Buba Galadima da ya daina nuna kansa da cewa shine sakataten amintattu na jam’iyyar daga yanzu.
A jawabinsa na karbar mulki a matsayin shugaban riko, Dr. Major ya yi alkawarin tafiyar da harkokin jam’iyyar bisa doka kuma ya sha alwashin cewa ba zai bai wa majalisar kunya ba.
Kwankwaso dai shi ne dan takarar Jam’iyyar NNPP a zaben 2023 da ya gudana.
Jam’iyyar ta kasance cikin rikici tun bayan kammala babban zaben 2023 inda bangarori daban-daban ke ta zargin juna a cikinsu.
Rikicin na cikin gida ya haifar da dakatar da jigon Jam’iyyar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na tsawon watanni shida.
Idan za a tuna dai NWC na jam’iyyar a ranar Alhamis 24 ga watan Agustan ya dakakatar da wanda ya kafa jam’iyyar Dr Boniface Aniebonam da babban sakataren watsa labarai na Jam’iyyar da wasu tun da farko, sai dai majalisar amintattu Jam’iyyar ya ki amincewa da dakatarwar da aka yi musu