Ɗaya daga cikin ‘yan kwamitin amintattu na Jam’iyyar NNPP, Injiniya Buba Galadima, ya ƙaryata batun cewa jam’iyyar ta dakatar da jagoranta, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Buba Galadima ya bayyana cewa, wasu korarrun ‘yan jam’iyyar da aka kora ne, suka kitsa batun korar jagoran da nufin yin juyin mulkin siyasa a jam’iyyar.
Buba Galadima wanda ya yi bayanin haka a Shirin Siyasa A Yau na Gidan Talabijin na Channels mai taken “Politics Today”, har ila yau ya ce uwar jam’iyyar ba ta da masaniya, “sai yanzu nake jin cewa wai an dakatar da Sanata Rabi’u Kwankwaso a bakinka. Magana ce da ake yin ta a Social Media kawai. Kuma maganar Social Media tamkar wasan kwaikwayon Nollywood ne da Kannywood.
“Su waɗanda aka riga aka kora, su Boniface Aniegbonam su ne suka kitsa wannan…. Sannan abin da suka yi zargi na ganawar Sanata Kwankwaso da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, Kwankwaso bai je ba sai da ya ji ta bakin dukkan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.”, In ji shi.
Rigimar jam’iyyar ta ƙara ƙazancewa ne yayin da tsagin Kwankwaso ya fitar da sanarwar korar Shugaban Kwamitin Amintattu kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar, Dakta Boniface Aniegbonam, a jiya Litinin.
Har ila yau, tsagin na Kwankwaso ya kori Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar, Agbo Major da kuma Tope Aluko bisa zargin cin amanar jam’iyyar.