Gwamna Uba Sani ya nuna farin cikinshi yayin da yake kaddamar da fara rabon sabbin kayan aiki na fasaha da aka siyo don inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko (PHCs) guda 290 a jihar Kaduna.Â
Gwamnan ya bayyana cewa, hakan na cikin alkawuran da suka dauka na farfadowa da inganta ayyukan cibiyoyin Kula da Lafiya na matakin Farko don inganta harkokin lafiya ga al’ummar jihar Kaduna.
“Bukatarmu a bangaren kiwon lafiya a matakin farko, ba wai raba kayan aiki ba ne kadai, za mu inganta fasahar ma’aikatan ta hanyar horarwa ta yadda za su yi fice a fanninsu, su bada ingantacciyar Kula ga marasa lafiya.
“Mun bada fifikon kulawa ga cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko fiye da sauran, sabida su ne ke cikin Unguwanni 255 da ake da su a fadin jihar kuma su suke fara yaki da cututtuka da ke damun jama’a, don haka, in sun inganta, cibiyoyin kiwon lafiya matsakaita da manya za su samu saukin cunkoson jama’a.” inji Uba Sani
Gwamna Uba Sani ya yaba wa Hukumar Kula da Kayayyakin Kiwon Lafiya ta Jihar Kaduna (KADHSMA) da Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kaduna (KSPHCB) da suka yi aiki ka-fada-ka-fada don ganin an kaddamar da fara raba kayayyakin don ci gaban al’ummar jihar.
“Abun godiya da jin dadi ne a gare ni yau, ganin na kaddamar fara rabon kayayyakin fasaha ga cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 290 da aka inganta a jihar Kaduna. Ina godiya a gareku.” Inji Gwamna Uba