Gwamnatin jihar Legas ta ce, za ta fara jigilar fasinjoji akan layin dogo na Blue Line a ranar Litinin 4 ga watan Satumba.
Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na sada zumunta, ya ce, za a fara gudanar da jigilar fasinja a ranar 5 ga watan Satumba daga karfe 6:30 zuwa 10 na safe da kuma karfe 4:00 zuwa 9:30 na yamma. Jirgin zai fara da yin zagaye 12 ne har na tsawon makonni biyu, har akai lokacin da zai dinga yin zagaye 76 a kowace rana.
“Akwai kyamarorin tsaro sama da 300 da aka dasa suna kula da jirgin tare da kyamarori sama da 30 suna lura da layin dogon kawai, akwai kananun tashoshin jirgin akan hanya da ke lura da duk motsin jirgin akan hanyar.
Anata bangaren, Manajan Darakta ta Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Legas (LAMATA), Misis Abimbola Akinajo, wacce ta fara gudanar da gwajin aikin jirgin tare da manema labarai, ta ce idan aka yi nazari a kan yadda aka tsara yanayin jigilar fasinjojin, Jirgin zai rika jigilar Fasinjoji 175,000 a kan titin a kullum.
Ta ce, duk da cewa, an tsara fara gudanar da jigilar fasinjoji tun a kwatan farko na shekarar 2023, amma sai aka jinkirta don tabbatar da cewa an samar da dukkan tsare-tsare da abunda ya kamata.
Ta ce layin dogo na Blue Line yana da kananan tashoshi biyar, wadanda suka hada da Marina, National Theatre, Orile-Iganmu, Alaba, da Mil 2.