A yau Alhamis 31 ga watan Agusta za’a raba jadawalin kofin zakarun turai na kakar wasa ta 2022 zuwa 2024.
Gasar ita ce karo ta 56, za a raba jadawalin ne a birnin Monaco dake kasar Faransa kuma an fara buga gasar ne tun a shekara ta 1955 zuwa 1956.
Za’a buga wasan karshe na wannan kakar a filin wasa na Wembley dake birnin London din kasar Ingila kuma shi ne karo na uku da za a buga wasan karshe a filin tun da aka canjawa gasar suna.
Ga jerin kasashen da suke da wakilai a gasar ta bana:
Ingila: Arsenal, Manchester City, Manchester United, Newcastle
Spaniya: Atletico Madrid, Barcelona, Real Madrid, Real Sociedad, Sevilla
Jamus: Bayern Munich, Borussia Dortmund, RB Leipzig, Union Berlin
Italiya: Inter Milan, Lazio, AC Milan, Napoli
Faransa: Paris Saint-Germain, Lens
Portugal: Porto, Benfica, Braga
Holland: Feyenoord, PSV
Austria: Red Bull Salzburg
Scotland: Celtic
Serbia: Red Star Belgrade
Ukraine: Shakhtar Donetsk
Switzerland: Young Boys
Turkey: Galatasaray
Belgium: Antwerp
Denmark: Copenhagen
Yadda Za a raba jadawalin
Tukunya ta 1: Manchester City, Sevilla, Bayern Munich, PSG, Barcelona, Benfica, Napoli and Feyenoord.
Tukunya ta 2: Real Madrid, Manchester United, Inter Milan, Borussia Dortmund, Atletico Madrid, RB Leipzig, Porto and Arsenal.
Tukunya ta 3: Shakhtar Donetsk, Salzburg, Milan, Lazio, Red Star, (Real Sociedad and Celtic (provisional teams)) (Draw not defined).
Tukunya ta 4: Lens, Newcastle, Union Berlin (Draw not defined)
Kungiyoyin da suka fito daga kasa daya ba zasu hadu ba a cikin rukuni a dokar
za’ a buga wasan karshe a filin wasa na Wembley dake London a ranar daya ga watan Yuni na shekara ta 2024.
kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ce dai ta lashe kofin a kakar data gabata.
Kungiyoyi 23 ne suka taba lashe gasar a tarihi kuma Real Madrid ce ta fi kowacce kungiya lashe kofin inda take da guda 14 ciki har da na farko da aka fara bugawa.