Kungiyar kwallon kafa ta Al-Ittihad na shirin biyan fam miliyan 118 don sayen dan wasa Mohamed Salah, duk da cewa Liverpool ta ce ɗan wasan ba na sayarwa ba ne.
Rahotanni sun bayyana cewa Kociyan kungiyar, Jurgen Klopp zai iya barin kungiyar idan Liverpool ta karɓi tayin Al-Ittihad ta Saudiyya a kan Salah.
A farkon wannan shekarar ne dai Salah ya sake sabon kwantiragi da kungiyar na tsawon shekara 3 sai dai neman da kungiyar ta Al-Ittihad take yiwa dan wasan yasa ake ganin zai iya canja shawarar komawa kasar Saudiyya da buga wasa.
A wannan Bazarar kungiyoyin Saudiyya da dama dai sun kashe kudi wajen sayan manyan ‘yan wasa daga nahiyar turai irin su Karim Benzema da Kante da Mendy da Mahrez da sauran su.
A gobe Juma’a, daya ga wannan watan na Agusta ne dai za’a rufe kasuwar siye da siyar da ‘yan wasa a manyan gasannin nahiyar turai.