Gwamnatin tarayya ta baiwa ko wacce jiha Naira biliyan biyu ciki har da Abuja daga cikin Naira biliyan biyar na tallafi da gwamnatin ta sanar a kwanan baya za ta baiwa Gwamnoni domin rage radadin cire tallafin mai.
Ministan kudi da tattalin arzikin kasa, Wale Edun ne ya shaida wa manema labarai hakan a Abuja.
Edun ya ce, wadannan kudaden, ba sa daga cikin kudin da gwamnatin ke son karbo wa rance na dala miliyan 800 daga Bankin duniya domin rage radadin cire tallafin man.
A cewarsa, gwamnatin ba ta son fitar da kudaden tallafin a lokaci daya, inda hakan ya sa ta dakatar da tura sauran Naira biliyan Ukun don kauce wa kara hauhawar farashin kayan masarufi.