A gabanin yanke hukuncin da kotun sauraron korafe-korafen zaben da ke zaman ta a Kano, magoya bayan jam’iyyar APC sun bayyana cewa addu’ar da suke ba ta riya ba ce, don haka suka ce ta su ba irin ta sauran ba ce.
Mashawarci na musamman kan harkokin gyaran motoci, Alhaji Idris Hassan ne ya bayyana haka a lokacin taron addu’ar da aka gudanar a unguwar Gwagwarwa da ke yankin karamar hukumar Nasarawa, inda ya ce magoya bayan jam’iyyar APC suna cikin nutsuwa kuma a wajen Allah suke neman nasara ba wurin kowa ba.
- Xi Ya Taya Wata Jami’a Murnar Cika Shekaru 70 Da Kafuwa, Sannan Zai Ba Da Jawabi A Yayin Bikin Bude CIFTIS Na 2023
- Abubuwa Takwas Da Gwamnatin Tinubu Za Ta Bai Wa Fifiko
Ya kara da cewa jama’ar Jihar Kano na nadamar abin da ya faru a lokacin zaben da ya gabata, musamman ganin yadda wannan gwamnatin ke yi wa harkokin ci gaban Kano dibar karan mahaukaciya.
“Babu shakka mu muna da cikakkiyar tarbiyar da muke mutunta na gaba da mu, muna kira da goya bayan Dakta Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakinsa Alhaji Murtala Sule Garo su ci gaba da hakuri.”
Shi ma da yake gabatar da nasa jawabin a wurin taron addu’ar, tsohon daraktan hukuma Zakka da Khubusi na Jihar Kano, Alhaji Safiyanu Ibrahim Abubakar Gwagwarwa (Tafidan Gwagwarwa), ya bayyana cewa, “Muna tawassili da sunayen Allah mai tsarki da alkur’aninsa, muna kuma da yakin cewa wanda muke neman a wurinsa wadataccen sarki ne, yana amasa tsarkakkiyar addu’ar da ba riya a cikinta, wannan ta sa mu idan za mu yi addu’a tsakaninmu da mahaliccin muke yi, ba wai tallata abubuwan da ya kamata ba.”
Tafidan na Gwagwarwa ya kuma yi tsokaci kan Sallar Alkunut da Gwamnatin Kwankwasiyya ta gudanar, inda ya ce wannan ba haka Allah ya ce a yi sallatul hajati ba, “A ina aka ce limamin irin wannan sallah ya yi huduba, sannan ya kama banbadanci tare da aibata wasu jama’a, don haka muna da yakinin sun ruguza kansu a wurin wanda ya kamata a ce an kyautatawa ayyuka ba a yi domin riya ba.”