Akwai sirruka da dama da ya kamata a ce uwargida ta san su ta kuma yi koyi da su; wadannan sirrika sun hada da tsafta, ladabi, biyayya, iya Magana, sai kuma uwa gaisuwa.
Za mu fi daura wannan maudu’i kan gaisuwa ne. Wanda gaisuwar nan fa ta kunshi abu biyu da suka hada da gaisuwar tambayar ya aka ta shi wato ina kwana, Allah ya tsare a dawo lafiya, sannan akwai gaisuwar sannu da dawowa.
- An Rufe Kasuwar Saye Da Sayarwar ‘Yan Wasan Kwallon Kafa Ta Bana A Turai
- Goyon Bayan Da Amurka Ta Baiwa Japan Game Da Zubar Da Ruwan Dagwalon Nukiliya Cikin Teku Ba Shi Da Amfani
Uwargida ko kinsan cewa sirrin da ke tattare da ina kwan, sannu da dawowa?
Idan ba ki sani ba, to bari ki ji. Idan gari ya waye kika yi sallar Asuba, juya ki ce wa maigidanki ina kwana ko ba ki yi dogon gaisuwa ba, sannan ki sauke nauyin shiga kitcin, ki hada abun kari. Bayan kin gama, ya ci ya kimtsa, raka shi bakin kofa bi shi da a dawo lafiya Allah ya tsare. Uwargida ke kanki a wannan ranan sai kin ji sauyi a zamantakewarku. Bayan ya dawo, sannu da zuwa ya zama kalmar farko.
Da yawan mata akwai abun da ba su fahimta ba wajen gaishe da miji wanda yake kara wa mace daraja da kima, sannan hakan na kara sa miji ya sake tabbatar da irin ingantacciyar tarbiyar da aka ba ki a gidansu.
Haka zalika, gaishe da miji yana sa uwargida ta kasance ko laifi ta yi masa ya kan yi kokari ya danne zuciyarsa wajen ganin ya daga miki kafa.
Kalmar sannu da dawowa, in dai kin rike wannan kalma, to za mu iya kiransa da ‘sirrin mallaka’, yana dawowa ki kasance bakinki ya zama kalmar sannu da dawowa shi ne abu na farko da zai furta. Amma wasu mata ka fin su ce komai, kora fi ne abun da zai fara fita a bakinsu, wanda hakan ba tarbiyya ba ne.
Ko da dai ana cewa gaisuwa al’ada ce, amma Hausawa na cewa ‘yaba kyauta tukwici’, idan aka duba komin zafi, ruwa, iska miji zai fita ya nemo abun da za ku ci ke da yara, to ashe in har zai yi muku wannan kokarin ke kuma matsayinki na uwar al’umma wacce aka fi sani da tausayi da sanin ya kamata, sai ki yi kokarin nuna tausayawanki a kansa. Kalmar sannu da dawowa a gareshi zai kara masa kwarin giwa wajen nemo muku abin sawa a bakin salati. Amma wasu matan miji na shigo za a fara ba shi bayanin maggi ko shiri ko manja ya kare.
Ta bangaren ‘ya’ya kuwa, yi kokari ki nuna musu tausayin ubansu ta hanyar koya musu gaisuwa da kuma sannu da zuwa. Idan kika yi kokari kika nuna musu hakan, ko cikin mutane sai kin ji ana yabon ‘ya’yanki, kuma shi ma mijin a duk sanda zai fita zai kassnce cikin kwarin gwiwa da annashuwa. Uwargida an san cewa tsakanin harshe da hakori ma ana sabawa, saboda haka tsakanin ma’aurata ma ana samun sabani, to amma kar ki bari bacin rai ya yi tasiri a zuciyarki, ki yi kokari ko fada kuka yi ki kasance mai dadin kalamai ga mai gidanki.