Batun kara shigo da sabbin mambobi, ya zama batun mai jawo hankalin bangarorin daban-daban, a gun taron kolin kungiyar BRICS da ya kammala.
A shekarar 2017, a karon farko Sin ta gabatar da ra’ayin hadin kai mai salon BRICS+, matakin da ya habaka dandalin BRICS, kuma ya jawo hankalin kasashe masu tasowa, wajen kara yin mu’ammala da hadin kai.
Shugaban kasar Comoros Azali Assoumani, wanda ke rike da ragamar shugabancin karba-karba na AU, ya shaidawa manema labarai na CMG cewa, lokacin da aka gudanar da wannan taro, kasashen Afirka sun yi iyakacin kokarin shiga tsarin gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban, kuma zarafin na su ya zo kan gaba.
Ya ce habaka mambobin BRICS, mataki ne mai kyau, kuma da yake yanzu an shiga karni na hadin kai, kamata ya yi a yi hadin gwiwa don tinkarar kalubaloli tare.
Azali Assoumani, ya kuma godewa alkawarin da Sin ta dade tana yi na goyon bayan Afirka, tare da godewa shugaba Xi Jinping. Kana ya yi fatan kara hadin kai da kasar Sin, a matsayin mataki dake matukar kara zurfafa huldarsu.
Yayin zantawar ta su, Azali Assoumani ya ce, Sin ta dade tana taimakawa kasashen Afirka gwagwadon karfinta, a fannin raya masana’antu, da zamanintar da sha’anin gona, da horas da kwararru da dai sauransu, matakin da ya taimakawa nahiyar wajen daga karfinsa na samun bunkasuwa ta bai daya, da yiwa masana’antu kwaskwarima. (Amina Xu)