Kungiyar Likitoci (ARD) na asibitin kwararru ta jihar Kogi (KSSH), Lokoja, ta jawo hankalin gwamnatin jihar dangane da karewar wa’adin kwanaki 21 da ta bai wa gwamnatin jihar da ta cika musu bukatunsu.
Kamfanin dillacin labarai ta kasa (NAN) ta labarto cewa kungiyar a ranar 9 ga Agustan ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin kwanaki 21 da ta cika musu bukatunsu ko kuma su tsunduma yajin aikin sai baabaa ta gani kamar yadda uwar kungiyar Liktoci ta kasa (NARD) ta umarta.
Wa’adin kwanakin dama ce da aka bude wa gwamnatin da ta hau teburin sulhu da sasantawa da kungiyar domin lalubo bakin zaren matsalolin.
A wata sanarwar hadin guiwa da shugaban kungiyar likitoci ARD KSSH, Dakta Ameh Friday da babban sakataren kungiyar, Dakta Peter Samuel tare da rabar wa ‘yan jarida a ranar Asabar a Lokoja.
Sun ce, matakin tafiya yajin aikin sun dauka ne domin tursasa gwamnati ta biya musu bukatunsu.
Daga cikin bukatun da likitocin ke da shi a wajen gwamnatin sun hada da sake nazartar CONMESS na 2014 zuwa CONMESS 2023, da amincewa da kudaden horaswa na MRTF 2020, 2021, 2022 da na 2023.
Alawus-alawu na shiga hatsara, aiwatar da matakan karin girma, da basukan da suke bi hade da sauran bukatu na daga cikin korafe-korafen likitocin.
Kungiyar ta nuna takaicinta na cewa gwamnatin jihar ba ta gamsuwa da nuna godiya kai kokarinsu ta hanyar yin halin ko-in-kula da tulin bukatunsu.
Don haka kungiyar ta ARD ta ce za ta gudanar da taro daga yau zuwa nan da kwanaki bakwai domin sanar da matakin dauka kan shiga yajin aikin.