“Tattalin arzikin duniya yana bunkasa idan an bude, kuma yana raguwa idan an rufe shi.” A yayin da yake jawabi ta kafar bidiyo ga taron baje kolin kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2023, game da hada hadar cinikayyar ba da hidima ko CIFTIS, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi nuni da cewa, zurfafa bunkasuwar hadin gwiwar cinikayyar ba da hidima da masana’antar hidima “ya sanya kuzari wajen inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya, da maido da martabar tattalin arzikin duniya, da kuma karfafa karfin ci gaban tattalin arzikin duniya.”
Shekarar da muke ciki shekara ce ta cika shekaru 45 da kasar Sin ta yi gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje. A matsayin wani muhimmin dandali na bude kofa ga kasashen waje na kasar Sin, bikin baje kolin na CIFTIS ya shaida irin gudunmawar da kasar Sin ta bayar kan ci gaban cinikayyar ba da hidima da bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Kristalina Georgieva, shugabar asusun ba da lamuni na duniya, ta bayyana kwanan nan cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana ba da gudummawar kashi daya bisa uku ga ci gaban tattalin arzikin duniya.
Ana iya hasashen cewa, bisa ga inganta zamanintarwa iri na kasar Sin, kasar za ta karfafa da fadada bude kofa ga kasashen waje. A cikin wannan yunkurin kuma, za a kara samar da ingantattun hidimomi irin na kasar Sin, wanda zai kawo karin fa’ida ga jama’ar duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)