Sergio Ramos na tattaunawa kan yiwuwar komawa Sevilla, a cewar majiyoyi.
Ramos, mai shekaru 37, ya kasance bai da kungiya tun lokacin da kwantiraginsa na Paris Saint-Germain ya kare a watan Yuli.
- Firimiyar Bana:Wasanni Uku Da Za Su Fi Daukar Hankalin Masu Kallo
- PSG Ta Karbi Aron Goncalo Ramos Daga Benfica
Tsohon mai tsaron baya na Real Madrid ya ja hankalin kungiyoyin Saudi Arabiya Al Ittihad, Galatasaray, FC Porto da wasu kungiyoyi a MLS, in ji majiyoyin, amma ya zabi Sevilla saboda ya fi son zama kusa da gida.
Sevilla ta lashe gasar cin kofin Europa a watan Mayu kuma ta yi rashin nasara a wannan kakar gasar ta La Liga, inda ta yi rashin nasara a dukkan wasanni ukun da ta buga inta take kasan teburi.