Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta bayyana cewa ta bankado wata makarkashiya da wasu mutane suke shiryawa ta gudanar da zanga-zangar tayar da tarzoma a fadin kasar nan don bata sunan gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro.
Idan dai ba a manta ba a karshen makon da ya gabata ne shugaba Bola Tinubu ya umurci hukumomin tsaro da su kwato duk wasu basussukan da ke da alaka da shirin Anchor Borrowers na babban bankin Nijeriya CBN.
- Manoman Tumatur 70,000 Na Bukatar Tallafin Gwamnatin Kano – Yadakwari
- CBN Ya Kara Kudin Ruwa Mafi Tsada A Cikin Shekara 22
LEADERSHIP ta ruwaito cewa shugaban ya bayar da umarnin ne bayan bincike ya nuna cewa kimanin N577bn daga cikin jimillar N1,103,793,587,359,070.00 da aka bayar saboda har yanzu ba a dawo da kudaden ba.
Bincike ya nuna cewa wasu daga cikin wadanda suka kasa biyan rancen sun hada da gwamnatocin jihohi, daidaikun mutane da kungiyoyin manoma da cibiyoyin hada-hadar kudi yayin da wasu suka yi kokarin dawo da kudaden da suka karba, wasu kuma suka gaza yin hakan.
Sai dai a wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar ta DSS, Dr Peter Afunanya, a ranar Litinin din nan, hukumar ta ce: “Rahotannin leken asiri sun nuna cewa wadanda suka shirya makircin sun hada da wasu ‘yan siyasa da kungiyoyin matasa da kuma kungiyoyin da ba na gwamnati ba.”
“Saboda haka, an shawarci mataimakan shugabannin jami’o’i da shugabannin manyan makarantu da su hana dalibansu shiga cikin rudanin da za su kawo wa jama’a cikas ta fuskar zaman lafiya.
“kazalika, an umurci iyaye da masu kula da su da su rika yi wa ‘ya’yansu da na unguwanni gargadi da su nisanta kansu daga shiga munanan dabi’u ko kuma sabawa doka da oda.