Da aka tambaye ta a yayin taron manema labarai da aka saba yi a yau 4 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin tana bin ka’idoji guda uku na mutunta juna, da zaman lafiya cikin lumana, da hadin kai irin na samun nasara tare, wanda shugaban kasar Xi Jinping ya gabatar a matsayin babban tushe wajen tafiyar da dangantakar dake tsakaninta da kasar Amurka, kana da himmatuwa wajen kafa ingantacciyar hanyar zaman tare tsakanin manyan kasashe tare da Amurka, da kuma ba da goyon baya da karfafa mu’amalar jama’a tsakanin kasashen biyu.
A baya-bayan nan, shugaba Xi Jinping ya rubuta amsar wasika ga “Kungiyar musanya tsakanin dalibai matasa na Amurka da Sin” dake jihar Washington da abokan hulda daga bangarori daban-daban ta Amurka, da jikan Janar Joseph Stilwell na kasar, wanda ya haifar da kyakkyawan ra’ayi a Sin, Amurka, da sauran al’ummomin duniya. Game da haka, jami’ar ta bayyana cewa, wasikun guda biyu sun nuna cewa, shugaba Xi Jinping ya dora mahimmanci sosai wajen sa kaimi ga yin mu’amala tsakanin jama’ar kasashen biyu.
Baya ga haka, jami’ar ta jaddada cewa, a cikin shekaru 40 da suka gabata tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Amurka, musaya tsakanin jama’a ta kasance wani abin da ba zai wuce gona da iri ba wajen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. (Mai fassara: Bilkisu Xin)