Gwamnatin tarayya a ranar Litinin ta bukaci kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da ta dakatar da shirinta na shiga yajin aikin gama gari na kwanaki biyu a matsayin gargari.
Ministan kwadago da ayyuka, Simon Lalong ne ya yi wannan rokon a yayin da ya ke ganawa da ‘yan jarida a Abuja.
NLC dai za ta shiga yajin aikin gargadin ne domin nuna fushinta kan yadda gwamnatin tarayya ta kasa cimma bukatun da aka gabatar kan halin kunci da matsatsin da al’ummar kasa ke ciki sakamakon janye tallafin mai.
Sai dai ministan ya ce gwamnati na kan kokarin magance matsalolin da suka addabi ma’aikata da al’ummar Nijeriya, ya bukaci a kara wa gwamnatin lokaci domin ta kammala aiwatar da tsare-tsaren samar da tallafin rage radadi.
Ya kuma tabbatar wa ma’aikata cewa gwamnati ba za ta taba watsi da su ba kuma ba za ta yaudaresu ba domin nuna godiya kan gudunmawarsu da sadaukarwarsu.
Kodayake ma ya ce har yanzu ma’aikatarsa ba ta amshi wasikar da ke sanar mata NLC za ta shiga yajin aikin ba kamar yadda doka ya tanadar, amma ya ce nan da ‘yan makonni za a sanar da wasu karin tallafi.
Ya ce tun da gwamnati ta dukufa wajen kyautata rayuwar ‘yan kasa akwai bukatar sake nazari kan yajin aikin.