Rundunar ‘Yatnsandan jihar Kaduna, ta ce jami’anta sun ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su a unguwar Kuriga Wussa da ke karamar hukumar Zariya a jihar.
Mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.
- Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin ‘Yansanda 3 A Kaduna
- ‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 21, Sun Kama 780, Sun Kwato Makamai 1,408 A Kaduna
Mansir ya ce jami’an ‘yansanda sun gudanar da aikin kai daukin ne a ranar Asabar.
A cewarsa, an samu nasarar ne sakamakon wani sintiri da suka kai a yankin Galadimawa na karamar hukumar Giwa.
“Jami’an ‘yansanda da ’yan banga na yankin sun shiga cikin dajin, lamarin da ya tilasta wa masu garkuwa da mutanen barin wadanda mutanen da suka sace, suka tsere zuwa cikin daji.”
Mansir ya ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna, Mista Musa Garba, ya yi kira ga jama’a da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana a kan alhakin da ya rataya a wuyansu na bai wa ‘yan sanda sahihin bayanai, domin tsaro ya shafi kowa da kowa.
Ya kuma ce rundunar ta himmatu da yin aiki tukuru a kowane lokaci don kare rayuka da dukiyoyin mazauna jihar Kaduna.