Huhumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta kama wasu da take zargi da hannu a karkatar da tallafin rage radadi da aka samar domin tallfawa al’umma.
DSS ta ce ta dauki matakin ne bayan samun rahotonni daga gwamnatocin wasu jihohi dangane da batun da ke da alaka da sama da fadi ko sayar da kayayyakin tallafin da aka samar domin taimakon al’umma.
Kakakin DSS, Dakta Peter Afunanya, shi ne ya shaida hakan a wata sanarwar da ya fitar a ranar Talata.
Ya ce bayan bincike da aka yi, an kama wasu da ake zargi da aikata laifuka a jihar Nasarawa da ke da hannu wajen karkatar da kayayyakin abinci da aka tanadar wa marasa galihu a jihar.
Dr Afunanya ya kara da cewa hakan ya sa sun gudanar da bincike kan batun kuma kawo yanzu sun kwato wasu kayayyakin ma.
Daga cikin wadanda aka kama ake zargi wasu jami’an hukumar samar da agajin gaggawa ta jihar Nasarawa (NASEMA) ne da abokan cin burminsu a kasuwanni, musamman kasuwar Modern da ke Lafia inda aka sayar da wasu kayan a can.
DSS ta kara da cewa an mika wadanda ake zargi zuwa inda ya dace domin daukan matakan ladaftarwa.
Hukumar Tsaron Farin Kayan sai ta yi kira ga al’umman kasa da su sanya ido su kuma kai rahoton duk wani kayan da suke zargi ga hukumomin tsaro mafi kusa da su domin daukan matakan gaggawa.