Sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Gabon sun saki hambararren shugaban kasar Ali Bongo daga kullen cikin gida da suka yi masa tun bayan hambarar da Gwamnatinsa a ranar Larabar makon da ya gabata.
Sojojin kuma, sun baiwa Bongo damar fita wajen kasar domin duba lafiyarsa.
Kakakin rundunar sojin kasar, Col Ulrich Manfoumbi ne ya sanar da ‘yancin Bongo a wata sanarwa da ya yi a gidan talabijin na kasar a yammacin Laraba.
Manfoumbi ya ce, an yanke shawarar ba Bongo ‘yanci ne sabida “yanayin lafiyarsa”, ya kara da cewa, “idan ya ga dama, zai iya fita kasashen waje don duba lafiyarsa,” in ji shi.
Bongo yana kan karagar mulkin kasar ne tun a shekarar 2009, lokacin da ya gaji mahaifinsa wanda ya shafe shekaru 41 yana mulkin kasar.