A ko ina a fadin Duniya, harkar saye da sayar da karafuna (‘Yan Kyadi ko ‘yan gwangwani) harka ce mai kawo alhairai masu yawa. A wani kiyasin da aka yi, bayani ya nuna ana samun fiye da Dala Biliyan 70 a harkar saye da sayar da karafuna a duniya a duk shekara.
A bayanin da kungiyar masu safarar karafuna da masu tattara da bola ta kasa (NASWDEN) suka yi, harkar masu Gyadi na tallafa wa harkokin sana’o’in al’umma a Nijeriya na fiye da Naira Tiriliya 1 a duk shekara.
- Yadda Tinubu Ya Yi Nasara Kan Abokan Hamayyarsa Atiku Da Obi
- Gwarzon Ɗan Ƙwallon Duniya Ta Ballon D’or: Yaushe Za A Bayar Kuma Wa Zai Lashe?
An kafa kungiyar NASWDEN mai akalla mambobi fiye da mutum 35,000 a johihi 36 na kasar nan, an kafa ta ne a shekarar 2005 da nufin daidaita ayyukan dillalai da dukkan masu hada-hada a bangaren tattaro karafa da abubuwa a bola wadanda ake sake sarrafa su don fitar da wasu abubuwan amfani ga al’umma. Duk da harkokin kasuwanci yana tafiya daidai ga masu wannan sana’ar, sai dai a halin yanzu sana’ar na fuskantar wata babbar barazana saboda wasu bata gari sun shiga cikin harkokin sana’ar inda suke neman bata sana’ar ta hanyar saye da sayar da kayayyakin sata.
A cikin wata uku da suke wuce an samu rahottanni fiye da dozin na yadda jami’an tsaro suke kama manyan motoci shake da karafunan hanyar jirgin kasa a kusan dukkan sassan kasar nan. Wannan zai sanya mutum ya yanke hukuncin cewa, lallai akwai wasu da ke Shirin durkusar da zirga-zirgar jirgin kasa ta hanyar satar karafunan hanyar jiragen kasar ana sayar da su da sunan gyadi. Abin ya zama a duk mako sai wata rundunar tsaro ta bayar da rahoton kama mota shake da karafunan hanyar jirgi ko wasu karafunan da jirgin kasa ke amfani da shi.
Rahoton na wadanda aka kama ne a kan hanyarsu amma daga dukkan alamu ba za a rasa wasu manyan motocin dauke da irin wadanna kayan da suka samu nasarar tsallakewa ba. Satar kayayyakin hukumar jiragen kasa wani abu ne da aka yi shekaru ana tafkawa amma bambancin a halin yanzu shi ne yadda lamarin yake faruwa ba kakkautawa, hakan kuma na bayar da matukar tsoro.
A kwanan nan ne, ranar 29 ga watan Agusta 2023, jami’an sojoji da ke aiki a karkashin shirin nan na ‘Operation Safe Haben’ da kuma ‘Hakorin Damisa IB’ suka bayar da rahoton kama wata babbar mota shake da karafunan jiragen kasa, an kama su ne a kan hanyar kauyen Gidan Ado da ke karamar hukumar Riyom ta Jihar Filato. Kwanaki 12 kafin wannan kamun kuma hukumar tsaron farin kaya ta (NSCDC) ta sanar da kama babbar mota kirar DAF dauke da karafunan hanyar jirgi an lullube su da wasu karafunan daban. A ranar 14 ga watan Agusta aka yi wannan kamun, an samu nasarar cafke mutum 4 da suka yi shigar Baban Bola. Haka kuma bayani ya nuna cewa, hukumar NSCDC ta samu nasarar cafke mutum 12 da ake zargi da laifin barnatar da karafunan hanyar jirgi, da ke a kan hanyar Kafanchan zuwa Kwai a Jihar Kaduna, da hanyar jirgin da aka shinfida a tsakanin Agwan zuwa kauyen Kuje a yankin Abuja da kuma na Nasarawa zuwa sansanin ‘yan yi wa kasa hidima (NYSC) da ke a kan hanyar Keffi zuwa Abuja. Haka kuma a ranar 7 ga watan Yuli rundunar ‘yansanda na Jihar inugu ta bayar da rahoton kama mutum biyu da ake zargi da barnatar da kayayyakin hukumar jiragen kasa, an kama barayin ne a garin Emene da ke kan babbar hanyar Inugu zuwa Abakaliki. A ranar 5 ga watan Yuli 2023 rundunar hukumar NSCDC ta samu nasarar kama manyan motoci 2 dauke da karafunan hanyar jirgi a garin Olooru da ke Jihar Kwara an samu nasarar kama mutum 6 da ake zargi a kan hanyarsu ta dawowa daga kauyen Jagundi ta karamar hukumar Kafanchan ta Jihar Kaduna.
Haka kuma a ranar 15 ga watan Yuni a garin Doma ta Jihar Nasarawa Sojoji sun samu nasarar kama mutum 12 da ake zargi da lallata tare da sace karafunan hanyar jirin kasa a Angwan Yara da Agyaragu a karamar hukumar Keana ta Jihar Nasarawa. Jami’n hulda da jama’a na runduna ta musamman ta 4 da ke Doma ya bayyana cewa, wadanda ake zargin sun yi ta kokarin ba sojojin cin hanci, inda har suka bayar da Naira Miliyan 5 don su kauce wa kamun sojojin.
Akwai rahotanni da dama na yadda barayin karafunan jirgi ke kokarin ba jami’an tsaro cin hanci don a bar su su wuce a kan hanyoyinmu. A ra’ayinmu bai isa kawai rahotannin kamun barayin karafunan hanyar jirgin kasa da ake yi ba, ya kamata jami’an staro su kara zurfafa bincikensu don gano masu kitsa harkar sace-sacen da ake yi da kuma wadanda suke a kan gaba wajen sayen karafunan. Ba za a iya samun nasara a wajen wannan kokarin ba sai an samu hadin kan kungiyar dillalai da masu saye da sayar da kyadi na kasa da kuma kungiyar masu motoci na kasa. In har wannan lamarin ya ci gaba a haka, nan gaba kadan ba za a samu karafuna hanyar jiragen kasar ba a sassan kasar nan wanda hakan zai mautukar shafar ci gaba da bunkasar tattalin arzikin kasa. Saboda haka dole a dauki matakin kawo karshen wannan mummunan aikin.
Akwai masu harkar saye da sayar da karafuna na gaskiya a sassan Nijeriya musamman a jihohin Ogun, Legas, Filato da Ribas. Saboda haka akwai bukatar su fito su kare sana’arsu kafin a ci gaba da danganta sana’ar Kyadi da sata. Nijeriya ta ci bashin makudan kudade don inganta harkokin zirga-zirgan jirgin kasa a ‘yan shekarun nan. Hanyar jirgi daga Abuja zuwa Kaduna mai stawon kilomita 187 ya lakume kusan Dala Biliyan 1, na Legas zuwa Ibadan mai tsawon kilomita 312 ya lakume Dala Biliyan 1.2 yayin da aka kashe Dala Biliyan 1.1 don samar da hanyar jirgin daga Kano zuwa Kaduna. Ana kuma bukatar fiye da Dala Biliyan 4 don hada hanyar jirgi daga Legas zuwa Kalaba wanda zai biyo ta Warri da Fatakwal. Ba zai yiwu gwamnati ta ci gaba da ciwo bashi don samar da ababen more rayuwa ba amma ana ci gaba da barnata su.