Ministan ayyuka, Dave Umani, ya dakatar da wasu ayyukan hanyoyi da ake yi a yankin Kudu Maso Gabas har sai an bibiyi kwangilolin da suke kasa da kuma wadanda za a kara bayarwa.
Umahi ya bayar da umarnin ne a ranar Alhamis a garin Enugu yayin da yake duba wasu ayyukan da ake ginawa da wadanda ake yi wa kwaskwarima da wasu hanyoyi da gwamnatin tarayya ke yi a yankin kudu Maso Gabas.
- Hukuncin Zaben Shugaban Kasa: Dimokuradiyya Ce Da ‘Yan Nijeriya Suka Yi Nasara – Buhari
- Tinubu Ya Umarci Jakadun Nijeriya Da Su Dawo Gida
Ministan ya nuna takaicinsa kan yadda ya ga wasu gadoji hudu da wasu aiyukan kilomita uku da su lakume kudi har naira biliyan 15.
“Na umarci daraktocin ma’aikatata da su zauna tare da ‘yan kwangila su sake nazarin aikin.
“Na ui imanin babu ta yadda za a yi aikin nan ya lashe mana kudin da ya wuce biliyan uku ko hudu.”
Kazalika, Ministan ya yaba kan yadda wasu ‘Yan kwangila suke gudanar da ayyuka masu nagarta a Enugu, ya ce duk da haka ya dakatar da biyan wasu kudaden kwangila har sai an zauna an sake bibiya da duba kudaden da aka ware musu.