Kamfanin tace man fetur mafi girma na kasar Sin wato Sinopec, ya bayyana a jiya Laraba cewa, ya fara aikin hakar rijiyar makamashi daga karfin turiri mai tsawon mita dubu 5, a birnin Haikou dake lardin Hainan na kudancin kasar Sin. A cewar kamfanin Sinopec, rijiyar za ta kasance rijiyar makamashi daga karfin turiri mafi zurfi a kasar.
A cewar Sinopec, makamashin turiri, makamashi ne na zafi da ake samu a cikin tarin duwatsu, da ruwa-ruwa da turirin duwatsu.
Ana iya kasa shi zuwa sassa uku: na farko shi ne albarkatun makamashin turiri mara zurfi, da ruwa mai zafi da kuma busasshen dutse mai zafi. An kiyasta cewa, yawan albarkatun busassun duwatsu dake da zafi da ke kasar Sin, ya kai kimanin tan triliyan 856 na makamashin kwal. (Ibrahim)