Lionel Messi ya jefa kwallo yayin da kasarsa Ajantina ta fara samun nasara a gasar cin kofin duniya ta Kudancin Amurka a ranar Alhamis bayan da ta doke Ecuador 1-0 a gida.
Tauraron dan kwallon na Inter Miami, wanda ya jagoranci kasar Ajantina a gasar cin kofin duniya karo na uku da aka yi a Qatar a watan Disambar da ya gabata, ya sake nuna kwarewarsa inda ya zura kwallo a ragar Ecuador.
- Wane Ne Arda Guler Mai Lakabin ‘Sabon Messi A Real Madrid’?
- “Kaunar Messi” Ya Nunawa Duniya Ainihin Kyawun Kasar Sin
Abinda yasa kasar Ajantina ta samu nasara akan abokiyar karawarta a wasan share fagen buga kofin Duniya.
Lautaro Martinez ya samu bugun tazara a cikin minti na 78 da fara wasa inda Messi yayi amfani da damarsa ya kuma zura kwallo a ragar Hernan Galindez.
Da kwallon Messi ya cimma tsohon abokin wasansa a Barcelona Luis Suarez na Uruguay a matsayin wanda ya fi kowa zura kwallo a raga a wasannin neman tikitin shiga kofin Duniya na kudancin Amurka da kwallaye 29.