Wata takarda da manyan ofisoshin kwamitin kolin JKS da majalisar gudanarwar kasar suka fitar, sun nuna cewa, za a karfafa hanyoyin shiga kasuwa, da inganta wuraren hakar ma’adanai da ma tsarin kula da harkokin tsaro.
Haka kuma, kasar Sin za ta dakatar da gina sabbin wuraren hakar ma’adinan kwal dake da karfin samar da kasa da tan dubu 900 a shekara, da kiyayen faruwar hadarin fashewar kwal da iskar gas, ko kuma matsalar da ta shafi yanayin ruwa. Baya ga rufe wuraren hakar ma’adinan da suka kasa cimma ka’idoji na tsaro da aka gindaya.
Takardar ta kara da cewa, za a karfafa hadin gwiwa da sayan wuraren da ba na hakar ma’adinan kwal ba, za kuma a zamanantar, tare da samar da na’urori masu sarrafa kansu, a wuraren hakar ma’adinai. (Ibrahim Yaya)