• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wata Girgizar Kasa Mai Karfi Ta Kashe Fiye Da Mutum 820 A Morocco

by Muhammad
2 years ago
Girgizar kasa

Wani rahoto da TRT Afrika Hausa ta rawaito ya ce, akalla mutum 820 ne suka mutu sakamakon mummunar girgizar kasar da ta faru a Maroko ranar Juma’a, a cewar ma’aikatar cikin gida ta kasar.

Gidan talbijin na Moroko, wanda ya ambato ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar tana bayyana haka, ya kara da cewa mutum 672 ne suka jikkata sakamakon girgizar kasar mai karfin maki 7.0 da ta kassara yankuna da dama na kasar.

  • Girgizar Kasar Turkiyya: An Ceto Wata Yarinya Bayan Shafe Awa 178 A Cikin Baraguzai
  • Girgizar Kasa Ta Kashe Mutum 7, Mutane 60 Sun Bace A Kasar Ecuador 

Tun da farko wata sanarwa da ma’aikatar cikin gida ta kasar ta fitar da sanyin safiyar Asabar ta ce akalla mutum 296 ne suka mutum yayin da mutum 153 suka jikkata sakamakon girgizar kasar.

Girigizar kasar ta kuma lalata gine-gine yayin da mutane suka rika tserewa daga gidajensu cikin firgici.

“Rahoton wucin-gadi ya nuna cewa girgizar kasar ta kashe mutum 296 a larduna da biranen al-Haouz, Marrakesh, Ouarzazate, Azilal, Chichaoua da kuma Taroudant,” in ji sanarwar, wadda ta kara da cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

LABARAI MASU NASABA

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

Wasu bidiyoyi da aka rika watsawa a shafukan sada zumunta wadanda ba a tantance sahihancinsu ba sun nuna yadda gine-gine suka rika rushewa yayin da wasu suke girgiza. An ga mutane cikin dimuwa yayin da wasu suke fitowa daga baraguzan gine-gine.

“Mun ji wata mahaukaciyar girgiza. Daga nan na fahimci cewa girgizar kasa ce. Mutane sun fada cikin firgici da yamutsi. Yara suna ta kuka yayin da iyaye suka dimauce,” kamar yadda Abdelhak El Amrani, wani mazaunin Marrakesh ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP ta wayar tarho.

Hukumar da ke nazari kan girgizar kasa ta Amurka [USGS] ta ce bayanan farko sun nuna cewa girgizar kasar da ta auku a Maroko tana da karfin maki 6.8 kuma ta faru a nisan kilomita 18 daga karkashin kasa.

Ta ce girgizar kasar ta faru ne da misalin karfe 11:11 na dare a agogon kasar kuma ta fi kamari a yanki mai fadin kilomita 56.3 a yammacin Oukaimeden, fitaccen wurin yin wasan zamiya da ke Tsaunukan Atlas.

Kafofin watsa labaran Maroko sun ce girgizar kasar ita ce mafi karfi da kasar ta taba fuskanta a tarihinta.

An ji karar girgizar kasar a Algeria da ke makwabtaka da Maroko, ko da yake Jami’an Tsaron Algeria sun ce ba ta yi wata barna ba.

A 2004, akalla mutum 628 ne suka mutu yayin da 926 suka jikkata sakamakon girgizar kasar da ta auku a Al Hoceima da ke arewacin Maroko.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna
Labarai

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga
Labarai

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025
Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra
Labarai

Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

November 9, 2025
Next Post
Dalibai 4000 Ne Suka Shiga Noman Kayan Lambu Na Zamani – Dakta Bello

Farin Ciki Ya Lullube Manoma A Taraba Sakamakon Tashin Farashin Agushi

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025
Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025
NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.