Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa amincewa ya zama mataimakin duk wani dan takarar shugaban kasa zai haifar da rugujewar jam’iyyar NNPP.
Kwankwaso, ya bayyana hakan ne a wata Hira da manema labarai a ranar Asabar, yayin wani taron kaddamar da ofishin jam’iyyar NNPP da kuma ganawa da zababbun ‘ya’yan jam’iyyar na Jihar Gombe.
Ya ce ginshikin siyasarsa da ya gina tsawon shekaru da kuma dimbin gogewarsa da ya ke da ita a mukaman siyasa daban-daban a kasar nan ya taimaka wajen ganin jam’iyyar NNPP ta daukaka cikin kankanin lokaci.
Ya bayyana cewa da irin daukakar da jam’iyyar NNPP ta samu cikin kankanin lokaci, duk abin da zai kawo cikas wajen tsaya wa takarar sa na shugabanci a karkashin jam’iyyar zai haifar da rugujewar jam’iyyar.
Kwankwaso ya tabbatar da cewa jam’iyyarsa ta dade tana tattaunawa da jam’iyyar Labour (LP) domin yiwuwar hadewa amma babban abin da ya hana hadewar shi ne batun wanda zai zama dan takarar shugaban kasa.