Matakin da mahukunta Kasar Sweden suka dauka bari a koana Alkur’ani mai tsarki a watanni tara da suka gabata ya sanya kasar ta yi asarar kusa Dala Fam miliyan 200,000, a cewar wata yada labarai ta kasar.
Kona Alkur’ani da wani dan siyasar kasar dan asalin kasar Denmark ya yi Rasmus Paludan ya yi, da kuma wanda Salwan Momika, wani dan gudun hijirar Iraki dake zaune a Stockokolm ya yi, sun sa Sweden ta yi asarar miliyan 200,000 na kudin kasar wato Swedish Krona, daidai Fam miliyan 199,300, a cewar gidan rediyon Sberiges.
- NSCDC Ta Kama Barayin Kebur Da Suka Yi Shigar Injiniyoyi A Abuja
- …Ya Kashe Uwargidan Da Yake Yi Wa Hidima Da Mahaifiyarta Gami Da Tafka Sata
Wannan ayyuka namasha’a sun sa hukumomi sun tura ‘yansanda domin bayar da tsaro da kuma katse tsarin ci gaba da aikata hakan, in ji rahoton da gidan rediyon ya bayar.
Sweden da Denmark dai sun fuskanci gagrumin suka da Allah wai daga kasashen duniya sakamakon bayar da iznin kona Alkur’ani ga wasu mutane har ma da basu kariyar ‘yansanda.
Paludan shugaban jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayi ta Stram Kurs, ya kona kwafi na Alkur’ani a biranen Malmo Norrkoping, Jonkoping, da Stokholm, ciki har da wadanda ya kona a lokacin bikin Ista na shekarar da ta wuce.
Ranar 21 ga Yuni, ya kona Alkur’ani a wajen ofishin jakadancin Turkiyya dake Weden.
Momika ya ja hankali duniyamako daya, bayan haka, lokacin da kona Alkur’ani a wajen Masallaci a birnin Stockholm lokacin babbar Sallah.
Ranar 20 ga Yuli ya jefar da Alku’ani a wajen ofishin jakadancin Iraki dake Sewden tare da tutar Iraki ya kuma tattaka su.
Shima wani dan gudun hijirar Iraki Barhami Marijan, ya kona Alkur’ani a Angbybadet dake kusa da birnin Stockholm ranar 3 ga Agusta.
Haka kuma mommika ya sake kona Alkur’ani a wajen ofishin jakadancin Iran dake Sweden a farkon watan gusta, sannan ya sake konawa a a wajen masallacin Masallacin Stockholm a makon da ya gabaci lokacin.
Duk da yake wadannan ayyuka na rashin kirki suna zubar da kima kasar Sweden da kuma jefea jami’an tsaronta cikin hadari, hukumomin kasar sun ba wa Momika damar kona Alkur’ani mai tsarki.
Hukumomin tsaron kasar ta Sweden sun ce yanayin tsaron kasar ya tabarbare sakamako ba wa wasu mutane damar kona Alkur’ani mai tsarki.