An bayyana cewa Nijeriya na matukar bukatar shugaba jajirtacce, wanda zai ceto kasar daga kalubalen da ta ke ciki, wanda kuma yana da bukatar a bi shi da addu’a don samun nasara.
Shugaban kungigiyar Malamai Masana Ilimin Alkaluma ta Nijeriya Sheikh Habibi Abdullah Assufiyyu ne ya yi wannan Kira a lokacin gudanar da wata addu’ar neman zaman lafiya da ci gaba mai dorewa ga kasar nan, wanda ya gudana a Kano.
Daga nan sai Shaikh Assufiyyu ya yi nuni da cewa shi a nasa ganin, dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyar PDP, Kuma tsohon mataimaki shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ne ya dace da wannan mukami bisa la’akari da gogewarsa a harkar shugabanci.
Ya ce Alhaji Atiku Abubakar a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban kasa yana da kwarewa ta musamman da zai kawo karshen matsalar tsaro da kuma rashin aikin yi da ya addabi al’umma, musamman Matasa.
Daga karshe, ya yi kira ga al’ummar kasar da su zabi shugaba nagari mai kishin kasa Wanda zai ceto Kasar daga kangin da ta fada, kuma ‘yan kasa su bishi da addu’o’i na samun zaman lafiya.