Fasinjoji 11 sun rasu a wani sabon hadarin kwale-kwale da ya kife da jama’a a karamar hukumar Gurin Fufore da ke jihar Adamawa.
Dakta Suleiman Mohammed na hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Adamawa (ADSEMA) ya tabbatar wa da LEADERSHIP afkuwar lamarin, inda ya ce, fasinjoji 10 sun mutu sannan kuma an ceto 10.
A ranar Litinin, Dakta Suleiman ya tabbatar da cewa, fasinjojin da lamarin ya rutsa da su, mafi yawancinsu Manoma ne da kuma ‘yan biki akan hanyar dawowarsu daga taron bikin radin suna.
Dan majalisa mai wakiltar yankin, Hon. Umar Bobbo Ismail ya bayyana cewa, har yanzu ba a gano fasinjoji 10 da iftila’in ya rutsa da su ba.
Jami’in yada labarai na karamar hukumar Fufore Jangai Abdullahi ya bayyana cewa, masu aikin ceto na kan yin kokarinsu domin gano sauran gawarwakin fasinjojin.
Wannan iftila’in ya afku ne bayan kwana daya da wani hadarin na kwale-kwale wanda ya yi sanadiyar rasuwar fasinjoji 10 a kogin Njuwa da ke a yankin Rugange a karamar hukumar Yola ta kudu da ke jihar ta Adamawa.