Akalla mutane 15 ne bayanai suka tabbatar da cewa sun mutu, sakamakon kifewar wani jirgin ruwa sakamakon iska mai karfi a ranar Juma’a a jihar Adamawa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mutanen da suka hada mata da kananan yara sun fito ne daga garuruwan Njuwa Lake da Rugange, a yankin karamar hukumar Yola ta kudu.
- Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sun Koka Kan Kwararar ‘Yan Bindiga Zuwa Jihohinsu
- Brazil Ta Cire Sunan Antony Daga Tawagarta Saboda Zargin Dukan Budurwarsa
Shaidun gani idon sun ce kwale-kwalen na kan hanyarsa ta tafiya garin Yola da nufin cin kasuwa a ranar Juma’a, inda ya kife da su a kogin da ke yankin Rungange.
Gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, cikin wata sanarwar manema labarai, da jami’in yada labaransa, Humwashi Wonosikou, ya aike wa manema labarai ya jajanta wa iyalan mutanen da abin ya shafa.
“Na umarci mataimakiyaga da ta ziyarci yankin ta kuma kayyade adadin asarar da nufin taimaka wa iyalan mutanen da abin ya shafa.
“Ina wajen taron kungiyar gwamnonin Arewa masu Gabas a Maiduguri, amma zuciyata tana tare da ku, iyalai da jama’ar Adamawa a wannan mayuwacin hali, Allah ya jikansu ya musu rahma ya kuma bada hakurin rashinsu” in ji gwamna Fintiri.
Yanzu haka dai, cikin mutum 23 da ke jirgin, an ceto mutum takwas, yayin da 15 kuwa har kawo yanzu babu labarin su.