Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta damu matuka, tare da nuna rashin gamsuwa da sanarwar da kungiyar tarayyar Turai (EU) ta bayar ta kaddamar da wani bincike kan yadda gwamnatin Sin take ba da rangwame kan motocinta masu amfani da wutar lantarki.
Kakakin ya ce, kasar Sin ta yi imanin cewa, binciken da kungiyar EU ta gabatar, wata al’ada ce ta ba da kariya ga harkokin cinikayya, yana mai cewa, manufar binciken ita ce kare masana’antun EU da sunan takara mai adalci.
Ya kara da cewa, binciken zai yi matukar kawo cikas tare da gurbata masana’antun kera motoci da ma tsarin samar da kayayyaki na duniya, ciki har da na kungiyar EU, kuma zai yi mummunan tasiri kan alakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da EU. (Ibrahim)