Yau Jummaa, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira taron manema labarai, inda hukumar kididdigar kasar Sin ta gabatar da manyan alkaluman tattalin arziki na kasar na watan Agusta.
A cikin watan Agusta, masanaantu sun gaggauta aikin sarrafa kayayyaki, adadin karuwar ayyukan masanaantu ya kai kaso 4.5 bisa dari, adadin da ya karu da kaso 0.8 bisa dari idan aka kwatanta da na watan Yuli. Kana, sanaar hidima ta karu cikin sauri a watan Agusta, musamman ma a fannin hidima ta zamani. A sai daya kuma, shaanin sayar da kayayyaki a kasuwanni ya farfadowa, sayayyar hidima ta karu cikin sauri.
Bugu da kari, yanayin guraben aikin yi bai sauya ba, kuma adadin marasa aikin yi a birane ya kai kaso 5.2 bisa dari, adadin da ya ragu idan aka kwatanta da na watan Yuli. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)