Rundunar ‘yansandan Jihar Edo ta cafke wani dan Kasar Togo, Michael Agbalo, mai shekaru 35, bisa zargin kashe wani Maharazu Umar a wurin aiki.
An ce wanda ake zargin ya bai wa Umar kwangilar taimaka masa wajen aikin gine-gine a lokacin da aka samu rashin fahimtar juna bayan kammala aikin kuma ana cikin haka ne ya kashe wanda abolin aikin nasa.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Chidi Nwanbuzor, ya ce wani Clement Obagbikoko ne ya kai rahoto a ofishin ‘yansanda na Etete, Benin.
Obagbikoko ya ce ya dauki wanda ake zargin ne don gudanar da ayyukan gine-gine a harabarsa, inda daga baya wanda ake zargin ya kawo wanda abin ya shafa wurin aiki..
“Da suka kammala aikin ne sai aka biya shi, da aka tambaye shi inda Umar yake, sai ya amsa da cewa ya tafi, amma yayin da matar Clement ke duba aikin da misalin karfe 7 na dare, sai ta iske gawar Umar a cikin harabar gidan.
“Nan da nan muka kira wanda ake zargin ya zo gidan kuma aka kama shi,” ya kara da cewa kakakin rundunar ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa ya bugi mamacin ne da guduma, kuma ya fadi ya mutu, ya kara da cewa yanzu dai an ajiye gawar a dakin ajiye gawarwaki a asibiti.
Ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da shi gaban kotu.
A wata hira da ‘yan jarida, wanda ake zargin ya ce ya bai wa Umar kwangilar taimaka masa a aikinsa amma kuma ya kashe shi ne saboda sun samu rashin fahimta.