Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga malamai da daliban jami’ar Northeastern, da su ba da gudummawa yadda ya kamata, wajen farfado da yankin arewa maso gabashin kasar Sin, da ma zamanantar da kasar Sin baki daya.
Xi ya bayyana hakan ne, a cikin amsar wasikar da ya aika jiya Jumma’a, inda ya mika sakon taya jami’ar murnar cika shekaru 100 da kafuwa da mika gaisuwa ga ma’aikatan sassan jami’ar da dalibai da tsofaffin daliban jami’ar.
Shugaba Xi ya ce, tun daga lokacin da aka kafa jami’ar zuwa yanzu, ta yi nasarar horar da kwararru masu tarin yawa, tare da ba da gagarumar gudummawa ga kasa da ma al’ummarta.
Ya bayyana fatan cewa, jami’ar za ta iya samar da karin hazikai masu basira bisa manyan tsare-tsare na bukatun kasar, da fadada matsayinta na kasancewa a kan gaba a muhimman fannoni, da ci gaba da samar da babban sakamako a fannin binciken kimiyya. (Ibrahim)