Gwamna jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya sha alwashin sadaukar a da Albashinsa na wata-wata domin yakar ayyukan ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane a Mahaifarsa Duguri da ke karamar hukumar Alkaleri a jihar.
Gwamna Bala ya bayyana hakan ne da yammacin ranar Asabar a lokacin da ya kai ziyarar jajantawa dangane da garkuwa da aka yi da mutane 39 a Duguri da ke Alkaleri.
Bala Muhammad, ya jinjina tare da yaba wa hadakar jami’an ‘Yansanda, Sojoji, Jami’an tsaron farin kaya (DSS) da NSCDC tare da hadin guiwar mafarauta bisa ceto mutane 39 da aka yi garkuwa da su a garin Alkaleri.
Gwamna Muhammad ya ce, ya sadaukar da albashinsa na wata-wata ne domin a yi amfani da shi wajen gudanar da ayyukan ‘yan banga da kuma sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da yaki da ‘yan bindiga.
Gwamnan ya kuma sanar da bada kyautar Mashina guda 50 domin yin ayyukan sintiri, da kyautar naira Miliyan 10 ga kungiyar ‘yan banga, tare da naira miliyan biyu ga hakimai biyu da suke yankin domin tabbatar da dakile ‘yan ta’addan da ke garkuwa da mutane a yankin.
Da ya ke nasa jawabin, kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi CP Auwal Musa, ya ce, lokacin da suka samu rahoton an yi garkuwa da mutanen, nan take suka hada kai da sauran hukumomin tsaro da mafarauta inda suka kutsa kai dajin Yankari inda maboyar ‘yan ta’addan ta ke, “mun samu nasarar ceto dukkanin wadanda aka yi garkuwa da su, su 39, mun kashe ‘yan ta’adda 10 bayan fafatawa da su”.
Ya jinjina wa gwamnan jihar bisa goyon bayan da yake bayarwa na kyautata harkokin tsaro a jihar.