Labarin da muke samu yanzu-yanzu na nuna cewa an hana mataimakin Gwamnan jihar Edo, Comrade Philip Shaibu, shiga ofishinsa da ke Dennis Osadebey Avenue, wato fadar gwamnatin jihar da ke birnin Benin, babban birnin Jihar Edo.
Wannan wani abu ne da ke nuna yadda dangantaka ta ƙara tsami a tsakanin Gwamnan Jihar Edo Andrew Obaseki da mataimakin nasa, Shaibu.
Shaibu wanda ya tafi ofis da niyyar shiga domin gudanar da ayyuka kwatsam sai ya tarar da an kulle kofar shiga.
Mataimakin gwamnan da hadimansa sun shafe tsawon awa guda suna tunanin ko daga baya za a bude musu kofar ofishin amma hakan ya ci tura daga bisani dole suka juya.
Shaibu ya yi ta kiran Gwamnan jihar Andrew Obaseki a wayar salula amma bai samu damar magana da shu ba.
Majiyoyi sun shaida cewar Shaibu ya yi magana da kwamishinan ‘yansandan jihar da daraktan ‘yansandan ciki na (DSS) inda ya shaida musu yadda aka kulle masa ofis da hanasa shiga.
Mataimakin Gwamnan ya kira kwamandan tsaron gidan gwamnatin jihar SP Ibrahim Babatunde, inda ya tambaye shi da dalili hana shi shiga ofishinsa, sai ya amsa da cewa umarni ne daga sama. Ya kara da cewa babban jami’in tsaron Gwamna (CSO) Wabba Williams, shi ne ya fi kamata a nemo domin ya yi bayanin da ya dace.
Shaibu ya kira Williams inda ya yi alkawarin cewa yana zuwa amma har tsawon lokacin da mataimakin gwamnan ya shafe yana jira bai zo ba.
“Har zuwa yanzu, ban samu wata sanarwa a hukumance kan inda zan koma ba. Illa wadanda suke da bayanin su ne ma’aikatana. Ma’aikatan gwamnati na da bayanin a hukumance amma ni ba ni da shi. A daidai lokacin nan da nake magana da kai, ina tsaye a mashigar gidan gwamnatin,” Shaibu ya shaida a lokacin da aka jiyo shi yana waya da wani mutum da ba a gane waye ba.
A makon jiya, an ce a wata wasika daga ofishin shugaban ma’aikatan jihar, Anthony Okungbowa, da aka aike ga babban sakataren ofishin mataimakin Gwamnan, ta unarci Shaibu da ya koma sabon ofishinsa da ke lamba 7 Dennis Osadebey Avenue, GRA, a birnin Benin babban fadar jihar.
LEADERSHIP ta labarto cewa makonni biyu da suka gabata an hango alamin ofishin mataimakin gwamnan a wani sabon ofishi da ake son ya koma da ke da tazarar mitoci da fadar gwamnatin jihar, sai dai Shaibu ya nace kan cewa ba a sanar da shi cewa za a canza masa ofishi da fitar da shi daga fadar gwamnatin ba.