Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi da Shugaban kungiyar Heirs Holdings, Tony Elumelu da Uwargidan tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr. Toyin Saraki, da wasu fitattun ‘yan Nijeriya sun isa birnin New York na kasar Amurka don halartar taron majalisar dinkin duniya karo na 78.
Taron UNGA karo na 78 yana da taken: “Sake gina amana da dawo da haɗin kai a fadin duniya: inganta aiki kan muradun 2030 da bunkasa samar da ci gaba mai dorewa da samar da zaman lafiya da wadata.”
- Tinubu Ya Isa Birnin New York Don Halartar Taron Majalisar Dinkin Duniya A Karo Na Farko
- Kungiyar Kwadago (NLC) Na Shirin Tunduma Wani Sabon Yajin Aiki Mai Dogon Zango
Sauran fitattun ‘yan Nijeriya da suka je don halartar taron na Majalisar sun hada da mawaki Yemi Alade; Disc Jockey (DJ) Florence Otedola, wanda aka fi sani da DJ Cuppy; shahararriyar mawakiya kuma marubuciya, Ms. Karimot Odebode da Wakili na musamman na Majalisar Dinkin Duniya kuma babban sakatare mai kula da makamashi mai (SEforALL) Damilola Ogunbiyi.
Sanusi II ya halarci bikin nuna fina-finai da ‘Yarjejeniyar samar da SDGs’ da kuma wani taron tattaunawa da mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed.
Yemi Alade ya yi wasa a lokacin bude taron SDG Action karshen mako inda jakadan UNDP, GoodWill, Elumelu ya gana da shugaban kasar Laberiya George Weah yayin da Dokta Toyin Saraki ta halarci SDG Action Weekend.
An bude taron Majalisar Dinkin Duniya 78 a ranar Talata 5 ga watan Satumba tare da muhawara da za a fara ranar Talata 19 ga Satumba.
Zaman karo na 78 zai haska hanyar cinma muradun da aka tsara don cimma ajandar 2030 na muradun ci gaba mai dorewa (SDGs).
A taron koli na SDG da za a yi a ranar Litinin da Talata, shugabannin za su yi nazari kan aiwatar da ajandar 2030 da kuma 17 SDGs.