Mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano sun cimma matsayar nuna matukar godiyarsu ga dan Adaidaita Sahu, Auwalu Salisu, ta hanyar sadaukar da wani kaso daga cikin albashinsu zuwa gareshi domin nuna karamci kan halin gaskiya da mutuntaka da ya nuna.
Auwal mai shekaru 22 a duniya, ya tsinci naira miliyan 15 da wani dan kasuwar kasar Chadi ya manta da su a Keken Adaidaita dinsa bayan ya dauki hayarsa a jihar Kano.
‘Yan majalisun, sun bayyana cewa, sun dauki matakin karrama Auwalu ne domin koyar da Darasi ga sauran al’umma kan bin tafarkin gaskiya da rikon amana.
Kakakin majalisar dokokin jihar, Alhaji Isma’il Jibril Falgore, ya ce, majalisar za ta gayyaci dan adaidaitan domin ta mika masa kyautar da aka tara masa.
Wani makusancin iyalan Salisu, ya shaida cewar, duk da iyalan Salisu na fama da matsalar karancin tattalin arziki amma sun zabi su rike gaskiyarsu ta hanyar mayar da kudin ga dan kasuwar.