A ranar 18 ga wata, agogon wurin, mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng bi da bi ya gana da babban sakataren MDD Antonio Guterres da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a gefen babban taron MDD a birnin New York.
Yayin ganawarsa da Guterres, Han Zheng ya ce, kasar Sin za ta kasance mai samar da zaman lafiya a duniya, da ba gudummawa ga ci gaban duniya, da kuma kare tsarin kasa da kasa, da goyon bayan MDD wajen taka muhimmiyar rawa a harkokikn kasa da kasa.
Yayin ganawarsa da Blinken kuma, Han Zheng ya bayyana cewa, bunkasuwar kasar Sin wata dama ce maimakon kalubale, riba ce maimakon hadari ga Amurka, kuma bangarorin biyu za su iya cimma nasara tare da samun wadata tare. Kasar Sin na fatan kasar Amurka za ta kara yin kokari wajen kara fahimtar juna, da amincewa da juna, da hadin gwiwar moriyar juna, ta yadda za a maido da dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka kan hanyar da ta dace, ta yadda za ta amfanar da kasashen biyu da ma duniya baki daya.
A nasa bangaren, Blinken ya ce, Amurka na fatan kasar Sin za ta yi nasara, kuma za ta ci gaba da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, kuma tana fatan karfafa hulda da kasar Sin, da sarrafa bambance-bambance, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa, da raya dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin a kullum. (Yahaya)