Ministan wutar lantarki Adebayo Adelabu, ya lashi takobin samar da wutar lantarki mai karfin megawat 20,000 nan shekaru uku masu zuwa.
Adebayo ya bayyana hakan a ranar Talata a taron makamashi na kasar nan da ya gudana a jihar Legas.
- Babbar Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Kasa Ta Sake Lalacewa
- Na’urorin Tattara Wutar Lantarki Na TCN A Birnin Kebbi Sun Fashe
Ministan ya ce, ya duba matsalar wutar da Nijeriya ke fuskanta ya gano mafita akan matsalar, inda ya ce, ba wata aba ce da za a sha wahala wajen lalubo bakin zarenta ba, ba kamar yadda wasu ‘yan Nijeriya ke hasashe ba.
Ministan ya ce, har yanzu Nijeriya na kan ci gaba da samar da wutar lantarki mai karfin megawat 4,000, inda ya nanata cewa, gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu, za ta samar da wutar da karfinta zai karu sosai nan da shekarar 2026.