A cikin wannan satin ne aka dawo ci gaba da buga wasannin gasar cin kofin zakarun Turai na Champions League na kakar wasa ta shekarar 2023 zuwa 2024 da za’a buga wasan karshe a filin wasa na Wembley dake Landan ta Ingila.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City za ta yi kokarin kare kofin Champions League a makon nan, inda ta fara wasan rukuni da kungiyar Crbena Zbezda ranar Talata.
Manchester City wadda mai koyarwa Pep Guardiola ke jan ragama za ta wakilci Ingila tare da Arsenal da Manchester United da kuma Newcastle, wadda rabonta da gasar ya kai sama da shekara 20.
Kungiyar Newcastle United tana rukuni mai sarkakiya na shida, wanda ya hadar da kungiyoyin Paris St-Germain da AC Milan da kuma Borussia Dortmund, rukunin da ake kira “rukunin mutuwa”.
Manchester City na rukuni na uku da ake cewa ba za ta fuskanci kalubale ba, da ya kunshi RB Leipzig da Red Star Belgrade da kuma Young Boys sai Celtic, wadda ake ganin za ta iya zuwa zagayen gaba, tana rukunin da ya kunshi Feyenoord da Atletico Madrid da kuma Lazio.
Kungiyar da take fama da kalubale, wato Manchester United ta kece-raini a rukunin farko da ya kunshi Bayern Munich da FC Copenhagen ta kasar Denmark da kuma Galatasaray.
Arsenal tana rukunin da ya hadar da kungiyar da ta lashe gasar Europa League a kakar da ta wuce, wato kungiyar kwallon kafa ta Sebilla da kuma PSB Eindhoben da Lens ta kasar Faransa.
Sai dai a wannan karon tun bayan da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi suka nuna kansu a Turai da taka rawar gani a shekaru da yawa, sai gashi kakar bana ba su a Champions League.
Ronaldo shi ne na farko da ya koma kasar Saudi Arabia – yana kungiyar Al Nassr – shi kuwa Messi yana Amurka a Inter Miami, sai kuma fitattun ‘yan wasan da babu su a Champions League a kakar nan sun hada da dan kwallon Brazil, Neymar da dan kasar Faransa, Karim Benzema, wanda ya koma Al-Ittihad, shi kuwa Neymar na Al Hilal dukkansu a Saudi Arabia.
Ranakun Da Za A Buga Wasannin Champions League:
Ranar wasannin farko: 19 zuwa 20 ga watan Satumba. Ranar wasa na biyu: 3 zuwa 4 ga watan Oktoba. Ranar wasa na uku: 24 zuwa 25 ga watan Oktoba. Ranar wasa na hudu: 7 zuwa 8 ga watan Nuwamba. Ranar wasa na biyar: 28 zuwa 29 ga watan Nuwamba. Ranar wasa na shida: 12 zuwa 13 ga watan Disamba.
Wasannin zagayen ‘yan 16: 13 zuwa 14 da 20 zuwa 21 ga Fabraiirun shekara ta 2024 da kuma 5 zuwa 6 da 12 zuwa 13 ga watan Maris, sai wasannin dab da kusa da na karshe: 9 zuwa 10 da 16 zuwa 17 April.
A dai gasar ta bana ta kofin zakarun Turai da aka fara bugawa a wannan satin, za’a buga wasan dab da karshe a ranar 30 ga Afirilu da 1 ga watan Mayu da 7 zuwa 8 ga watan Mayu sai kuma wasan karshe da za’a buga ranar 1 ga watan Yuni.
An yi hasashen cewar Manchester City ce za ta kara lashe kofin Champions League ba wai Real Madrid ko Bayern Munich ba, in ji wata kididdiga daga Gracenote Euro Club Inded, wadda ke auna kokarin kungiyoyi a wasanninsu.
Manchester City tana da kaso 37 cikin 100 a damar lashe kofin, Real tana da kaso 13 cikin 100 da kuma Bayern mai kaso 11 cikin 100, haka kuma akwai damar wata sabuwar kungiyar ta lashe kofin da kaso 19 cikin 100.
Sannan Manchester City da Real Madrid da Bayern Munchen da kuma Barcelona, dukkansu suna da kaso 90 cikin 100 ta kai wa zagaye na biyu a wasannin gasar ta bana. Sannan wannan ce kakar karshe daga ita za a sauya fasalin wasannin kungiyoyi 32 ne aka raba su rukuni takaws dauke da hur-hudu kowanne, biyu da suka ja ragamar rukuni su kai zagaye na biyu zuwa kwata fainals da dab da karshe da karawar karshe, amma kuma daga kakar wasa ta 2024 zuwa 2025 kungiyoyi 36 ne za su kece raini a tsakaninsu.