Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Erik ten Hag ya ce ya gaji yanayi marar kyau a kungiyar kuma ya bayyana cewa yana fatan kawo karshen matsalolin da suka addabi kungiyar.
Wannan na zuwa ne bayan dan wasa Jadon Sancho ya yi atisaye shi kadai ba tare da tawagar Manchester ba har sai ya sasanta da kocin, bayan da Ten Hag ya ajiye Sancho a benci a wasan da Arsenal ta doke Manchester United 3-1 saboda a cewarsa Sancho ba ya nuna kwazo wajen atisaye.
Kocin ya ce an kawo shi Manchester United ne domin tabbatar da sauyi, yana mai cewa, ba aikinsa ba ne ya daidaita abubuwa sai domin dawo da kungiyar matsayin da aka santa a baya.
Erik ten Hag dai ya samu yabo wajen tabbatar da da’a a Old Trafford musamman yadda ya ajiye Cristiano Ronaldo da Marcus Rashford a benci a kakar da ta gabata saboda wasu dalilai daban.
Baya ga Sancho, Manchester na fama da matsaloli na ‘yan wasa saboda rauni musamman Raphael Barane da Luke Shaw da Mason Mount kodayake, Lisandro Martinez da Bictor Lindelof sun murmure. A satin da ya gabata ne Manchester United ta yi rashin nasara a hannun.
Brighton 3-1 a wasan mako na biyar a Premier League inda minti na 20 da fara wasa Brighton ta fara cin kwallo ta hannun Danny Welbeck, kuma kwallo ta hudu da ya zura a ragar United tsohuwar kungiyarsa.
Manchester United ta ci wasanni biyu a gida daga ukun da ta kara a bana kenan, shi ne wanda ta doke Wolberhampton da Nortingham Forest kuma kungiyar ta yi rashin nasara a gidan Tottenham da Arsenal – za kuma ta ziyarci Bunnley a gobe Asabar.